Hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) reshen jihar Ribas ta himmatu wajen fito da tsare-tsaren da suke saukakawa da shawo kan matsalolin da ake samu na jinkirin samar da fasfo domin kauce wa matsin lamba na bukatar fasfon.
NIS a karkashin jagorancin CIS James Sunday a jihar ta Ribas ta samar da littafin fasfot har guda 6,000 a cikin wata daya tak da ya taimaka sosai wajen rage tulin bukatun fasfo da jama’a ke gabatawa da kuma saukaka samar wa mutane da fasfo din.
Sabon jami’in kula da harkokin fasfo, mai mukamim mataimakin Kwanturola, Audi Musa Maisudan sa’ilin da ke bayani wa Kwanturolan hukumar na jihar, James Sunday a lokacin ziyarar aiki zuwa ofishin aikin fasfo da ke Mile 1 a garin Fatakwal, ya ce, sabon tsarin ya rage jinkirin da ake samu wajen samar wa jama’a da fasfon a lokacin da suka bukata.
A nasa bangaren, Kwanturola James Sunday, ya jinjina wa sabon jami’in tare da tawagarsa bisa himmar da suka nuna wajen biyayya ga umarnin ministan harkokin cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola da Kwanturol Janar na hukumar NIS, CGI Isah Jere Idris na cewa kada a bari samar wa jama’a da Fasfo ya zama abun damuwa ko wahala ga ‘yan Nijeriya.
Ya ce, umarnin ya taimaka matuka wajen saukaka hanyoyin da ake bi wajen samar da fasfon ta yadda ake biya wa masu bukatun fasfot din bukatun su ba tare da wani tarnaki ba.
A cewarsa, “Tsarin ya taimaka wajen rage koma baya da shan wahala, kuma duk mai bukata da ya bi ka’ida yana samun fasfo din sa a ranakun da aka gindaya wanda ya rage caza kwakwalwa, da kawo saukin aiki.”
“Na kawo ziyarar ce domin gani da idona kan ko an bi umarnin Minista da Kwanturola Janar, kuma na gamsu da yadda na ga Jami’ai sun dukufa wajen inganta aiki. Kuma dole ne a mutunta jama’a a samar musu da fasfo kan lokaci kuma bisa sauki ba tare da sai sun sha wahala ba.
“Mun kuma kwashi tsoffin hannu wadanda suka jima mun sauya musu sashi illa iyaka kwararrun da ake da bukatar aikinsu matuka, yin hakan zai ba da dama wadanda suka dace kuma suke da karsashin aikin su ne za su rika tafiyar da lamuran domin saukaka samar da fasfo ga jama’a.”
Daga bisani ya gargadi masu sako-sako da aiki ko kauce wa ka’idar aiki su shiga taitayinsu domin hukumar ta NIS ba za ta lamunci sakaci da aiki ba.