Kwanturola Janar na Hukumar Shige da Fice ta kasa NIS, CGI Isah Jere Idris MFR ya sanar da korar wasu jami’an hukumar su takwas (8) daga bakin aiki tare da hukunta wasu jami’an 18 da aka samu da aikata laifuka daban-daban da ya saba wa dokar hukumar don ladabtarwa.
Sanarwar ta biyo bayan amincewar Hukumar Gudanarwar Rundunonin da ke karkashin Ma’aikatar Cikin Gida (CDCFIB) wadda a njna cewa munanan ayyukan jami’an sun kasance abin da ma’aikatar ba za ta amince a ce jami’anta ne ke aikata irin wannan halayya ba.
In za a iya tunawa, jami’ai 35 ne ake tuhumarsu a wannan shekara, wadanda aka gabatar a gaban babban kwamitin ladabtarwa (SDC) da kuma na tabbatar da bin tsarin aiki (ORT) don tabbatar da tuhume-tuhume daban-daban na laifuffukan da suka shafi ladabtarwa wanda ake zarginsu da aikatawa, wadanda suka hada da cin zarafi abokan huldarsu, ayyukan Allah wadai, rashin gaskiya, barin wurin aiki ba tare da izinin hukumar ba (AWOL) da sauransu.
Bayan kammala binciken da kwamitocin suka yi, SDC da ORT, an kori jami’ai takwas da suka hada da Babban Sufiritanda na Shige da Fice (CSI), mataimakan Sufiritantanda na Shige da Fice (DSI) biyu, mataimakan Sufiritande na Shige da Fice II (ASI2) da kuma wasu Uku masu kananan mukami.
Bugu da kari, an umurci wani Babban Sufiritanda na Shige da Fice da ya yi takardar ritayar dole yayin da wasu jami’ai tara (9) aka rage musu mukami. Sun hada da Mataimakin Sufiritanda na Shige da Fice II (ASI2) wanda aka maida zuwa matsayin Sufeto na Shige da Fice; da Sufeto biyu da aka maida zuwa mukamin Mataimakin Sufeto; da wasu masu kananan mukamai su shida (6) da aka kwace mukamin da suke kai.
Sannan kuma, akwai wasu Jami’ai tara (9) da aka raba wa takardar gargadi, sun hada da Mataimakin Sufiritanda na Shige da Fice II (ASI2) da Kananan Ma’aikata takwas (8), sannan kwamitocin sun wanke wasu jami’ai shida (6) daga dukkan zarge-zargen da ake yi musu.
Bugu da kari, Kwanturola Janar din ya amince da sauya wa jami’ai 100 da aka tura filin jirgin sama na Legas wurin aiki nan take yayin da ya ba da umurnin tuhumar wasu don tabbatar da zargin da ake musu kan badakala a filin jirgin da aka ba da rahoto kwanan nan kana a san matakin da za a dauka akan su.
Kwanturolan Janar, na amfani da wannan damar don tabbatar wa ‘yan kasa da cewa, Hukumar NIS ba za ta lamunta duk wani hali ko nau’i na halin rashin gaskiya ba ga duk Jami’anta, don haka, yana kira ga jama’a da su ci gaba da bada rahoton duk wani nau’in hali na cin zarafi ko rashin gaskiya a bakin aiki da aka ga jami’in hukumar na aikatawa.