Gwamnatin tarayya ta ce, akalla Fasfo Miliyan 1.9 hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) ta samar a shekarar 2022 da ta gabata, da ke nuna an samu ci gaba da kusan kashi 80 cikin 100 kan wanda aka samar a 2021.
Ministan kula da harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ne ya shaida hakan a ranar Litinin yayin kaddamar da ofishin karba da shigar da bayanan Fasfo da ke Alimosho a Jihar Legas.
- Shugaba Buhari Ya Karrama CGI Isah Jere Da Lambar Yabo Ta Ƙasa Bisa Mutunta Ɗan’adam A Shugabancinsa
- Shugaban NIS Isah Jere Ya Sanar Da Ƙarin Girma Ga Jami’ai 4,526
An samar da ofishin ne a wani mataki na samar da dabarun tabbatar da aikin Fasfo don tafiya cikin sauki da hanzari ga ‘Yan Nijeriya.
Ministan ya kuma ce, hakan zai rage wahalhalun da ake sha wajen aikin Fasfo a Legas.
“Mun dukufa wajen fadada ayyukanmu na samar da Fasfo domin cike gibin karancin da ake yawan samu a manyan birane musamman irin su Legas. Wannan dalilin ne ya sanya aka samar da ofishin Fasfo a Alimosho da zai rage nauyi ga wasu ofisoshin Fasfo uku da suke Legas.”
Aregbesola ya kara da cewa, NIS na aiki tukuru wajen kara himma da azama a bangaren samar da Fasfo domin biyan bukatun masu nema da shawo kan matsalolin da ake fuskanta.
“Bukatun Fasfo na karuwa duk shekara sakamakon yadda ‘Yan Nijeriya da dama ke bukatar fita kasashen waje da kuma wadanda suke son mallakar Fasfo din a matsayin shaida.
“Amma mun kara yawan wuraren yin aikin. A shekarar da ta gabata mun kuma samar da Fasfo Miliyan 1.9, sabanin miliyan 1 da muka samar a 2021.”
Ministan ya yi karin hasken cewa ofishin da aka bude a Alimosho zai rika amsar zallar bukatun masu neman fasfo, amma ba wai waje ne da za a rika wallafa fasfon ba.
Duk da hakan ministan ya ce akwai bukatar kara samar da wasu ofisoshin yin Fasfo a kalla guda 15 a Legas sakamakon cewa jihar ita ce take da kusan rabin dukkan fasfon da ake gabatar da bukatar nema a Nijeriya.
Aregbesola ya kuma jadadda cewa babu makawa a shigar da kamfanoni masu zaman kansu wajen samar da wadannan ofisoshin na karba da shigar da bayanan fasfo a Legas, saboda kalubalen kudade da gwamnati ke fuskanta, domin hakan zai rage tsawon lokacin da ake kwashe wajen jiran fasfo.
“Amma saboda kalubalen kudade, gwamnati bata iya samar da wadannan ofisoshi, don haka za mu bukaci abokan hulda masu zaman kansu da za su samar da ofishin, abin da kawai za su yi shi ne samar da ofisoshin amma jami’an shige da fice ne za su rika kula da su tare da gudanar da su.
“Tabbas muna bukatar karin wannan a Legas. Hakan ya faru ne saboda rabin duk takardun fasfo ana yin su ne a Legas.”
Aregbesola ya kuma yi kira ga masu bukatar fasfo da su rika yi da kansu a ofisoshin NIS ba tare da mu’amala da marasa gaskiya ba.
Tun da farko dai, Aregbesola ya kaddamar da hedikwatar hukumar shige da fice ta Nijeriya (NIS) reshen Jihar Legas da ke Ikoyi.
Ya bayyana cewa kaddamar da ofishin na daya daga cikin ci gaban da ma’aikatar harkokin cikin gida ta samar a karkashin gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
“Tun da aka nada ni a matsayin minista, mun kaddamar da sabbin hedikwatocin jihohi 17 a fadin kasar nan na hukumar NIS, inda ta Legas ita ce ta 18.
Kokarin da gwamnatin Shugaba, Muhammadu Buhari, take yi na ganin an kara tabbatar da tsaron iyakokinmu ya sa aka samar da sabbin ofisoshi na kula da sintiri da inganta Tsarin Kula da Iyakoki na zamani bisa doka”. In ji shi.