Hukumar Shige Da Fice ta Nijeriya (NIS) ta samu gudunmawar na’urorin aiki na miliyoyin nairori daga Kamfanin IHS da ya yi shuhura a duniya wajen samar da kayan aiki na sadarwar zamani.
Kamfanin ya bai wa NIS na’urorin ne domin ƙara tsaurara tsaro a iyakokin ƙasa musamman ganin cewa Nijeriya tana fuskantar zaɓen 2023.

Babban Shugaban kamfanin, Dakta Mohammed Darwish wanda ya damƙa gudunmawar ga Shugaban NIS, CGI Isah Jere Idris MFR, a shalkwatar hukumar da ke Abuja a yau Litinin, ya bayyana cewa kamfaninsu ya jima yana aiki kafaɗa da kafaɗa da masana’antar sadarwa a Nijeriya sama da shekara 21 da suka gabata inda ya samar da aikin yi ga sama da ‘Yan Nijeriya dubu arba’in (40,000).
Tun da farko a nashi jawabin, CGI Isah Jere ya gode wa kamfanin bisa gudunmawar da suke bayarwa ta fuskar kyautata mu’amala da zumuncin aiki, kana ya tabbatar da cewa lallai ya fara haduwa da Kamfanin ne a sama da shekara 20 da suka gabata, lokacin da yake wakiltar kujerar NIS a Majalisar Bunƙasa Harkokin Zuba Jari ta Nijeriya.
CGI Isah Jere, kamar yadda sanarwar da Jami’in Sadarwa na NIS, Tony Akuneme ya fitar ga manema labarai ta ruwaito, ya yi alkawarin aiki da na’urorin kamar yadda ya dace musamman a halin yanzu da ake fuskantar zaɓe.

Kayayyakin sun haɗa da na’urorin Motorola guda 25, da na sadarwa na tafe da gidanka guda 155 da sauran wasu manyan kayan sadarwa.
Daga cikin tawagar NIS da suka tarbi mahukuntan Kamfanin na IHS akwai Mataimakiyar Kwanturola Janar mai kula da sha’anin kuɗi da harkokin mulki, Misis Caroline Adepoju da muƙaddashiyar mataimakiyar Kwanturola Janar, Dora Amahin da ke kula da bincike da tsare-tsare.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp