Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS), ta yi wa jami’anta sama da 60 karin girma zuwa matakai daban-daban.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar da yammacin ranar Juma’a jim kadan bayan kammala bikin karin girman ta yi wa jami’an.
- DSS Ta Bankado Shirin Boko Haram Na Kai Wa Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Hari
- “Akwai Masu Shekara 18 Zuwa 20 Ba Tare Da Hukunci Ba A Gidan Gyaran Hali Na Kuje”
Babban Kwanturola-Janar na NIS, CGIS Isah Jere Idris, ya yaba wa jami’an da aka yi wa karin girman.
“Ina yi wa kowa maraba da zuwa wannan muhimmin taro na kara wa jami’anmu karin girma.
“Karin girma wani nau’i ne na aiki tukuru, jajircewa da rikon amana a bakin aiki.
“A matsayinku na jami’an NIS ina jan hankalinku da zage damtse wajen aikinku kan yi wa kasarku hidima. Ku yi aikinku yadda ya dace musamman a zaben 2023. Ku kasance ‘yan ba ruwanku, ku yi aiki a tsanaki.”
Daga cikin wadanda hukumar ta yi wa karin girma har da kakakinta na kasa, Tony Akuneme wanda ya samu karin girma zuwa mukamin Kwanturola.
Akuneme na daga cikin manyan jami’ai 64 da hukumar NIS ta yi wa karin girma.
Akuneme ya fara aiki shekaru 30 da suka gabata a matsayin jami’in kadet, kuma ya yi aiki a sassa daban-daban da suka hada da Legas, Akwa Ibom, Birnin Tarayya, Babban Kwamishinan Nijeriya a Kasar Kanada da Hukumar Kula da ‘Yan Jaridu ta Nijeriya da dai sauransu.
Akalla Kwanturola 11 ne aka yi karin girma zuwa mukamin Mataimakin Kwanturola-Janar yayin da mataimakan Kwanturola 53 aka daga darajarsu zuwa kwanturolan kwastomomi.