• Leadership Hausa
Monday, October 2, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ba Zai Yiwu A Samu Hadarin Kaucewar Jiragen Kasa Da Yawa Daga Kan Layin Dogo A Lokaci Guda Ba

by CMG Hausa
8 months ago
in Daga Birnin Sin
0
Ba Zai Yiwu A Samu Hadarin Kaucewar Jiragen Kasa Da Yawa Daga Kan Layin Dogo A Lokaci Guda Ba
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

Birnin Hangzhou Ya Samu Karuwar Masu Yawon Bude Ido Albarkacin Gasar Wasanni Ta Asiya Dake Gudana

Shugaban Syria: Manyan Tsare-tsare Uku Na duniya Su Ne Jagororin Sabuwar Duniya

“Yadda ake samun kaucewar jiragen kasa da yawa daga kan layin dogo a lokaci guda, wannan abu ne da ba zai yiwu ba, dole ne akwai wani abu a kasa!” A shafukan sada zumunta na Amurka, mutane sun nuna shakku kan wannan batu daya bayan daya. A halin yanzu, hadarin “jirgin kasa dake dauke da sinadarai masu guba” da ya faru a Ohio na kasar Amurka yana ci gaba da jawo hankulan mutane, amma yayin da alummar yankin ke ci gaba da zaman fargaba da kuma mamakin aukuwar hakan, irin wannan hatsarin jirgin kasa ya afku daya bayan daya a Texas da South Carolina.

Sakamakon sabon binciken da Hukumar Kula da Sufuri ta Amurka ta fitar a ranar 14 ga wata, ya bayyana cewa, watakila an samu hadarin kaucewar jirgin kasa daga kan layin dogon a Ohio ne saboda zafin tsarin lura da sassan wilin jirgin kasan. Amma, a hakika, wannan hadarin jirgin kasa ya auku ne sakamakon kokarin neman riba mai yawa da kamfanin na layin dogo ke yi na tsawon shekaru, wanda ke haifar da tarin hadurra. Wannan ya kara nuna yadda dukkan tsarin layin dogo na Amurka ke neman moriya kawai amma ba tare da la’akari da saura ba. Haka ya fallasa manyan matsalolin ci gaba da ake da su.

A ganin manyan kamfanonin jiragen kasa masu jigilar kayayyaki na Amurka, aikin farko na layin dogo shi ne “kayan aiki na samun karin kudi”, amma ba “mahimman ababen more rayuwa” ba. Lokacin da tsarin jirgin kasa ya cika da “neman kudi”, to hadarin yana karuwa kuma nan da nan. Idan komai ya dogara da manufar samun riba, komai yawan tsare-tsaren ababen more rayuwa da Amurka ta gabatar, da kyar suke iya amfanar talakawa.

Ga ‘yan siyasar Amurka, idan ba su yi kwaskwarima sosai kan tsare-tsare ba, duk wani kyakkyawan tsarin samar da ababen more rayuwa ba shi da wani amfani, illa wata dabara ta karkatar da kasafin kudi zuwa aljihun manyan jamian kamfanoni. To, ta yaya za su ba da amsa kan Yadda Amurka ta zama haka? (Mai fassara: Bilkisu Xin)

ShareTweetSendShare
Previous Post

NIS Ta Yi Wa Jami’ai Sama 60 Karin Girma

Next Post

Ya Kimar Mace Mara Sana’a Take A Wurin Mijinta?

Related

Hangzhou
Daga Birnin Sin

Birnin Hangzhou Ya Samu Karuwar Masu Yawon Bude Ido Albarkacin Gasar Wasanni Ta Asiya Dake Gudana

4 hours ago
Syria
Daga Birnin Sin

Shugaban Syria: Manyan Tsare-tsare Uku Na duniya Su Ne Jagororin Sabuwar Duniya

5 hours ago
Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Ofishin Jakadancin Kasar Sin Dake Najeriya Ya Shirya Bikin Murnar Cikar Sin Shekaru 74 Da Kafuwa

6 hours ago
Amurka
Daga Birnin Sin

Amurka Ita Ce “Daular Karya”Ta Ko Wace Fuska

8 hours ago
’Yan Wasan Kasar Sin Sun Zarce Tsammani A Hangzhou 
Daga Birnin Sin

’Yan Wasan Kasar Sin Sun Zarce Tsammani A Hangzhou 

1 day ago
Za A Wallafa Sharhin Xi Kan Ciyar Da Zamanantar Da Kasar Sin Gaba
Daga Birnin Sin

Za A Wallafa Sharhin Xi Kan Ciyar Da Zamanantar Da Kasar Sin Gaba

1 day ago
Next Post
Ya Kimar Mace Mara Sana’a Take A Wurin Mijinta?

Ya Kimar Mace Mara Sana'a Take A Wurin Mijinta?

LABARAI MASU NASABA

Kotu A Amurka Ta Umarci Jami’ar Chicago Ta Bai Wa Atiku Bayanan Karatun Tinubu

Kotu A Amurka Ta Umarci Jami’ar Chicago Ta Bai Wa Atiku Bayanan Karatun Tinubu

October 1, 2023
Tinubu

Ranar ‘Yanci: Tinubu Ya Kara Wa Kananan Ma’aikata N25,000 Kan Albashinsu

October 1, 2023
Hangzhou

Birnin Hangzhou Ya Samu Karuwar Masu Yawon Bude Ido Albarkacin Gasar Wasanni Ta Asiya Dake Gudana

October 1, 2023
Syria

Shugaban Syria: Manyan Tsare-tsare Uku Na duniya Su Ne Jagororin Sabuwar Duniya

October 1, 2023
BUA

Daga Gobe 2 Ga Oktoba Farashin Buhun Simintin BUA Ya Koma N3,500 – Kamfanin

October 1, 2023
Kasar Sin

Ofishin Jakadancin Kasar Sin Dake Najeriya Ya Shirya Bikin Murnar Cikar Sin Shekaru 74 Da Kafuwa

October 1, 2023
Yadda ‘Arewa Peace Ambassador Forum’ Ta Nada Sheikh Muhajjadina Jakadan Zaman Lafiya

Yadda ‘Arewa Peace Ambassador Forum’ Ta Nada Sheikh Muhajjadina Jakadan Zaman Lafiya

October 1, 2023
Amurka

Amurka Ita Ce “Daular Karya”Ta Ko Wace Fuska

October 1, 2023
Gwamnatin Tarayya Ta Yaba Da Ayyukan Bello Koko Na Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kafa Sashi Na Musamman A NPA Don Inganta Ayyukanta

October 1, 2023
Dambe: An Fafata Tsakanin Dan Aliyu Da Rabe Shagon Ebola

Dambe: An Fafata Tsakanin Dan Aliyu Da Rabe Shagon Ebola

October 1, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.