Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), CGI Isah Idris Jere ya yi wa manyan jami’ai 94 da suka samu ƙarin girma ado da sababbin muƙamansu a shalkwatar hukumar da ke Abuja, yayin da ragowar huxun aka yi musu a Ma’aikatar Cikin Gida.
Wannan ya biyo bayan amincewa da ƙarin girma ga manyan jami’an ne da Hukumar Gudanarwar Rundunonin Ma’aikatar Cikin Gida (CDCFIB) ta yi tare da fitar da sunayen waxanda suka samu a shekarar 2022 a can kwanan baya.
Sanarwar da ta fito daga Jami’in hulxa da jama’a na NIS, ACI Amos Okpu ta bayyana cewa jimillar sabbin waxanda aka ƙara wa girma zuwa muƙamin ƙananan mataimakan Kwanturola Janar 24 da Kwanturololi 70 aka yi musu ado da sabbin muƙaman a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da ya samu halartar takwarorin NIS da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Cikin Gida da sauran manyan jagororin Hukumar CDCFIB.
Da yake jawabi a wurin, Shugaban NIS, Isah Jere ya bayyana cewa ƙarin girman da jami’an suka samu ya nuna ɓaro-ɓaro a fili irin yadda hukumar ta mayar da hankali ga inganta walwalar jami’anta. Ya nunar da cewa wannan yana daga cikin manyan ƙudurori uku da yake son cimmawa tun daga lokacin da ya karɓi ragamar shugabancin hukumar da suka haxa da inganta tsaron iyakokin ƙasa, gyarar fuska ga ayyukan fasfo sai kuma kyautata jin daxi da walwalar jami’ai.
Ya hori sabbin jami’an da suka samu ƙarin girman su ƙara duƙufa sosai ga aiki da kula da ayyukan na ƙasa da su domin tabbatar da ayyuka sun inganta a hukumar a samu xorewar ci gaban da ake samu. Ya ƙara da cewa, hukumar ba za ta lamunci raggonci ba daga gare su musamman ta ɓangaren da ake ganin ana iya cimma nasara xari bisa xari.
Tun da farko dai, Sakatariyar Hukumar Gudanarwa ta CDCFIB, Hajiya Aisha Rufa’i ta taya sabbin masu muƙaman murna bisa ci gaban da suka samu ta la’akari da cancanta, tana mai jaddada cewa hukumar ta yi nazari sosai a kan halaye da xabi’unsu, da ƙwazonsu na aiki da iya zance da sauran dabarun da ake buƙatar gani kafin a yi wa manyan jami’ai ƙarin girma.
Wakazalika, shi ma Kwamishinan Hukumar Gudanarwar mai kula da xaukar aiki da ƙarin girma, Manjo Janar Emmanuel Bassey mai ritaya, ya yi kira ga jami’an da aka ƙara wa girman su jagoranci sauran ma’aikata da ke ƙarƙashinsu cikin dattaku da kamun kai sannan a koyaushe ya zama suna cikin shirin aiki bisa ƙwarewa da xa’a a matsayinsu na manyan jami’ai.
Daga cikin manyan jami’an da aka saka musu sabbin muƙaman nasu na ƙananan mataimakan Kwanturola Janar akwai ACG Kemi Nandap, babbar jami’ar da ke kula da shige da fice a Filin Jiragen Sama na Murtala Muhammad da ke Legas, da babban jami’in harkokin ofishin CGI da aka sauya kwanan nan, ACG Ahmad Bauchi Aliyu da kuma Kwanturola Mustapha Ahmad, mataimaki na musamman ga CGI a fannin gudanar da ayyuka.
A halin da ake ciki kuma, Ministan Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola a ranar Talata ya sanya wa sababbin jami’ai da aka naxa a matsayin manyan mataimakan Kwanturola Janar muƙamansu, a babban xakin taro na ma’aikatar. Waxanda aka yi wa ado da muƙaman sun haxa da DCG Oluremi Talabi, DCG Josephine Kwazu, DCG Modupe Anyalechi da kuma DCG Muhammad Aminu Muhammad.
Ministan ya taya su murna a kan sabbin muƙaman nasu kana ya nemi su yi amfani da basirarsu da ƙwarewar aiki wajen yaƙi da rashin tsaro a ƙasar nan.
Daga cikin manyan mutanen da suka halarci bikin maƙala sabbin muƙaman na NIS akwai Kwamishinan Tarayya na Hukumar Gudanarwa ta CDCFIB, ACG Ado Jaffaru (mai ritaya), da Sanata Uba Sani, da Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna, Malam Bala Abbas Lawal, da wakilan shugabannin rundunonin da ke ƙarƙashin ma’aikatar cikin gida da sauransu.