Rahoton da hukumar kididdiga ta kasa NBS ta fitar ya nuna cewa, duk da cewa, Nijeriya ba ta mayar da hankali wajen hakar albarkatun Zinare da kuma sarrafa shi ba, fannin ya samar wa da Kasar kudin shiga naira biliyan 10.3 a kwatar farko ta shekarar 2022.
A cewar rahoton, ana fitar da Zinaren zuwa kasar Switzerland da Daular Larabawa inda hakan ya bai wa kasar samun kudaden shiga naira biliyan
10,057.83 da kuma naira biliyan 329.39.
Nijeriya na yin kokari wajen mayar da fannin na zamani wanda mafi yawanci masu hakarsa, suna yi ne hata haramtacciyar hanya da fasakwarinsa zuwa kasashen Ketare.
Duk da cewa, an gano Zinaren a jihohin kasar nan kamar su Zamfara, Kaduna, Kebbi, Niger, Kogi, Ogun, Osun Abuja, Bauchi, Cross River, Edo, Osun, Niger, Sokoto, Kebbi, Oyo, Ebonyi, Kwara, har yanzu Nijeriya ba ta da karfin sarrafa shi zuwa wasu nau’uka kamar su Awarwaro da Sarka.
A kwanan baya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, Nijeriya ta yi asarar dala biliyan 3 saboda fasakwaurin zinare da ake yi a tsakanin 2012 zuwa 2018.
An kuma kiyasta cewa, masu hakarsa ta haramtacciyar hanya, suna hakar tan 2 na Zinare a duk wata.
A jawabin Buhari a karon farko na sayar da Zinaren ya ce, shirin Zai taimaka wajen bunkasa ayyukan hakar Zinaren a Nijeriya wanda zai samar da ayyukan yi 250,000 da kuma samar wa da kasar dala miliyan 500 a duk shekara.