Ƙungiyar ƙwadago (NLC) ta ƙasa reshen jihar Kano ta gudanar da wata zazzafar zanga-zanga da safiyar yau Litinin a ofishin kamfanin rarraba wutar lantarki na KEDCO da kuma ofishin hukumar kula da wutar lantarki ta ƙasa (NERC) da ke Kano.
Sakataren NLC na jihar, Abbas Ibrahim, ya bayyana cewa; wannan matakin da suka dauka na zanga-zangar ya biyo bayan ƙarin kuɗin wutar lantarki da aka yi, wanda ƙungiyar ba za ta lamunta ba.
- Ƙungiyar Ƙwadago Ta NLC Na Zanga-zanga Kan Ƙarin Ƙudin Wutar Lantarki A Nijeriya
- Karancin Wuta: Nijeriya Za Ta Daina Sayar Wa Kasashen Ketare Wutar Lantarki
Ibrahim ya ce; ana gudanar da wannan zanga-zangar ne a duk jahohin Nijeriya baki ɗaya domin neman lallai a janye wannan ƙarin kuɗin wutar lantarki da aka yi, tare da mayar da farashin wutar kamar yadda yake a baya.
Sai dai kuma kamfanin na KEDCO har yanzu babu wata sanarwa ko martani da ya yi kan zanga-zangar. Watakila hakan na da nasaba da cewa matakin ƙarin kuɗin wutar ya faru ne a ƙasa baki ɗaya ba iya Kano ba.
Yanzu dai ido ya koma kan ministan wutar lantarki na ƙasa, Adebayo Adelabu, ko me zai ce game da kiraye-kirayen rage kuɗin wutar lantarkin da aka ƙara da kaso 300%.