Wani labari da BBC Hausa ta wallafa a shafinta ya ce, Kungiyar Ƙwadado ta Nijeriya NLC, ta zargi gwamnatin ƙasar da kitsa kai wa ‘ya’yanta hari a lokacin zanga-zangar da ƙungiyar ta shirya gudanarwa a faɗin ƙasar a ranakun 27 da 28 ga watan da muke ciki.
Cikin wata sanarwar da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugabanta na ƙasa, Comrade Joe Ajaero, NLC ta zargi gwamnatin ƙasar da shirya amfani da wata ƙungiyar farar hula mai suna ‘Nigeria Civil Society Forum’ (NCSF), wajen kai wa ‘ya’yanta hari a lokacin zanga-zangar lumanar da ta shirya gudanarwa.
- Kungiyar Kwadago (NLC) Na Shirin Tsunduma Wani Sabon Yajin Aiki Mai Dogon Zango
- NLC Na Neman A Biya Ma’aikata Naira Miliyan Ɗaya A Matsayin Sabon Mafi Ƙarancin Albashi
”NCSF na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da gwamnati ta ɗauki nauyinsu, kuma za ta yi amfani da su don kawo cikas ga zanga-zangar lumana da ‘ya’yan ƙungiyarmu suka shirya don nuna adawa da yunwar da ƙasarmu ke ciki”, in ji Comrade Ajaero.
Ƙungiyar ta ce tana son gwamnati ta fahimci cewa zalunci kan ‘ya’yanta ba shi ne zai yi maganin halin matsin tattalin arziki da yunwa da ƙasar ke ciki ba.
”Kamar yadda gwamnati ta yi a Minna da wasu biranen ƙasar, inda ta riƙa harba hayaƙi mai sai ƙwalla da dukan mata tare da kulle su, kawai don sun nuna damuwarsu kan yunwar da ke damunsu. Bai kamata a ɗauki nauyin wasu don hana mutane bayyana abin da ke damunsu ba. Bai kamata a tarwatsa waɗanda ke kukan yunwa da alburushi ko hayaƙi mai sa ƙwalla ba”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Ƙungiyar ta kuma jaddada aniyarta na gudanar da zanga-zangar da ta shirya yi a faɗin ƙasar a ranakun da ta tsara yinsa.
”A don haka NLC da sauran ƙawayenta za mu gudanar da zanga-zangar da muka shirya yi don nuna adawarmu kan tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki da rashin tsaro da ƙasarmu ke fuskanta”, in ji Ajaero.
”A matsayinmu na ‘yan ƙasa, muna da ‘yancin gudanar da zanga-zangar, kuma tarihi na nuna cewa a koyaushe zanga-zangarmu ta lumana ce, sai dai a inda gwamnati ta haddasa hargitsi”, in ji Ajaero.
A baya-bayan nan dai hukumomin ƙasar sun riƙa kira ga ƙungiyar kwadagon ta jingine zanga-zangar da ta shirya gudanarwa kan tsadar rayuwa a ƙasar.
Ko a makon da ya gabata ma hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta yi kira ga ƙungiyar NLCn ta dakatar da zanga-zangar saboda dalilai na tsaro.
Haka shi ma ministan shari’a na ƙasar Lateef Fagbemi, cikin wata wasiƙa da ya aike wa lauyan ƙungiyar kwadagon, Femi Falana, ya yi kira ga ƙungiyar ta jingine zanga-zangar da ta shirya yi a faɗin ƙasar.
To sai dai a cikin wasiƙar martani da lauyan ya aike wa ministan ya buƙace shi da samar da jami’an tsaron da za su bai wa ‘ya’yan ƙungiyar kariya a lokacin zanga-zangar lumanar.