Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC), ta buƙaci gwamnatin tarayya ta janye ƙudurorin gyaran dokar haraji da ke gaban majalisar dokoki, tana mai cewa hakan na da matuƙar muhimmanci don kare walwalar ma’aikatan Nijeriya.
A saƙonsa na sabuwar shekara ga ma’aikata da al’ummar Nijeriya, shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero, ya ce wannan buƙata ta taso ne saboda matsin da ƙarin haraji zai haifar wa rayuwar talakawa da ma’aikata.
- Ta Leko Ta Koma, An Cire Sunan Olmo Daga Jerin Yan Wasan Laliga
- Kudaden Shigar Sinima Na Kasar Sin A 2024 Ya Kai Yuan biliyan 42.5
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta riƙa gudanar da harkokinta cikin gaskiya da bayyanawa tare da tafiya da jama’a a duk wasu matakan da za ta ɗauka.
“A yayin da muke shiga shekarar 2025, muna taya ma’aikata da al’ummar Nijeriya murnar sabuwar shekara, tare da fatan samun kyakkyawar rayuwa da ci gaba a ƙasarmu,” in ji Ajaero.