Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC), ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da shirin ƙara kuɗin wutar lantarki ga masu amfani da layin A, B, da C.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi bayan taronta a Jihar Adamawa, NLC ta ce ba za ta yarda da shirin hukumar lantarki ta ƙasa (NERC) na sauya layin wuta ga kwastomomi da sunan inganta wutar lantarki ba.
- Hasashe Kan Tarukan CPPCC Da NPC Na 2025
- Majalisar CPPCC Za Ta Gudanar Da Taron Shekara-shekara Daga Ranar 4 Zuwa Ta 10 Ga Maris
“Ba komai ba ne illa yunƙurin ƙara wa mutane kuɗin wuta ba tare da sun shirya ba,” in ji sanarwar NLC.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa yanzu masu ƙarfi a ƙasar na ƙara jefa talakawa cikin ƙunci ta hanyar ƙarin haraji da kuɗin wuta, duk a daidai lokacin da tattalin arziƙin ƙasa ke cikin matsala.
Ta kuma yi barazanar shiga zanga-zanga idan har aka aiwatar da shirin ƙarin kuɗin lantarki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp