Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC), ta yi barazanar shiga yajin aiki a kasa baki daya daga tsakar daren ranar Talata, saboda gayyatar da ‘yansanda suka yi wa Shugabanta, Kwamared Joe Ajaero.Â
Wannan ya biyo bayan wani taron gaggawa da Kwamitin Zartarwa na Kasa na kungiyar (NEC), ya yi tare da Allah-wadai da zarge-zargen da ‘yansanda suka yi wa Ajaero, wanda suka hada da daukar nauyin ta’addanci da cin amanar kasa, inda suka ce ba su da tushe.
NEC ta jaddada cewa, duk da cewa NLC za ta amsa gayyatar ‘yansanda, hakan ba ya nufin amincewa da wadannan zarge-zarge ba.
NLC ta kuma yi tir da ci gaba da tsangwamar shugabanninta, inda ta bayyana hakan a matsayin yunkuri na kuntata wa kungiyar ta kwadago.
NEC ta umarci dukkanin rassan NLC na jihohi da su fara gangamin mambobinsu domin tafiya yajin aiki idan har wani abu ya samu Ajaero ko wasu shugabanninta.