Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC), ya bayyana cewa bai biya kudin tallafin man fetur ba cikin shekaru tara da suka gabata.Â
A cewar Babban Jami’in Kudi na kamfanin, Alhaji Umar Ajiya, ya ce kamfanin kawai yana kula da gibin farashin shigo da man fetur ne.
- Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Karuwar Zargin Cin Zarafi A Rundunar Sojojin Amurka
- Peng Liyuan Ta Gana Da Uwar Gidan Shugaban Vietnam
Ya jaddada cewa babu wani dillali da ya karbi kudin tallafi daga NNPC, wanda ya ce duk wani gibin kudi ana warware shi ne kai-tsaye tsakanin kamfanin da gwamnati.
Ajiya, ya yi bayani cewa gibin na faruwa ne saboda gwamnati tana umartar sayar da man fetur a farashi mai rahusa fiye da yadda ake sayo shi.
Dapi Segun, Mataimakin Shugaban Sashen Kasuwanci na NNPC, ya bayyana irin tsarin bashi da kamfanin samarwa dangane da man fetur.
Segun ya kuma bayyana cewa biyan bashin da ake bin ‘yan kasuwa yana sauyawa bisa ga yanayin hada-hadar kasuwanci, amma jaddada cewa abin da yafi muhimmanci shi ne tabbatar da ci gaba da samar da man fetur a fadin Nijeriya.
Idan ba a manta ba, a ranar Litinin ne aka wayi gari da wani rahoto da ke nuna cewar shugaba Tinubu ya bai wa NNPC umarnin biyan tallafin man fetur da ribar da kamfanin ya samu ta 2023.