Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya karyata zargin da wasu ke yi masa na cewa, wai wasu kamfanonin mai an kasashen waje ns binsa Dala Biliyan 6.
Babban jami’in watsa labarai na kamfanin NNPC, Olufemi Soneye, ya bayyana haka, ya kuma kara da cewa, duk da cewa, ana gudanar da harkokin kasuwancin danyen mai ne a tsarin bashi a kasuwannin kasashen waje amma kamfanin yana tafiyar da harkokinsa ne a bisa tsarin da ya fi karbuwa a sassan duniya kamar sauran ‘yan kasuwa.
- Mun Gano Hanyoyin Da Ake Satar Man Fetur A Nijeriya – NNPC
- NNPC Bai Fara Sayen Man Fetur Ɗinmu Ba – Matatar Dangote
Ya kuma ce, kamfanin NNPCL na sane da nauyin da ake kansa a masayin babbar kamfani da ta fito daga babbar kasa kamar Nijeriya.
Haka kuma, Soneye ya karyata masu cewa, NNPC bai bayar da kudaden da ake sa rai dag a asusun gwamnatin tarayya kamar yadda aka saba, ya ce, har yanzu NNPCL ne a kan gaba wajen zuba kudade a asusun gwamnatin tarayya wanda shi ne ake rabawa ga bangarorin gwamnati a duk wata.
Wannan bayani na NNPC ya biyo bayan rahotanin da ke cewa, wasu kamfanoni masu shigo da man fetur suna dari-dari kan ba NNPC bashin man fetur saboda rashin biyansu kudaden da suke bin NNPC din a baya.
Rahoton ya ce, kasancewar NNPC ne kadai doka ta ba damar shigo da man da fetur a Nijeriya amma yana amfani da wasu kamfanonin wajen shigo da man amma kuma ya tara musu bashin da ya kai dala biliyan 6.
Bayanin ya nuna cewa, a halin yanzu a kwai manyan jiragen ruwa dayuke da man fetur a gabar ruwan Nijeriya amma sun ki sauke wa saboda tsoron rashin biyan su kudaden da suke bi da ba a biya su ba.
Soneye ya karyata dukkan zarge-zargen, ya ce, suna nan suna kokarin fahimtar juma tsakanainsu da ‘yan kwangilarsu.