Mataimakin mai magana da yawun jam’iyyar PDP na kasa, Ibrahim Abdullahi, ya ce manyan ‘yan adawa uku a Nijeriya na tattaunawa kan yiwuwar hadewa da dunkulewa wuri daya domin ceto ‘yan Nijeriya daga yunwa da tabarbarewar tsaro gabanin zaben shugaban kasa na 2027.
Abdullahi ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da gidan talabijin din Channels a ranar Litinin.
- Muhimmin Sakon Kwankwaso Ga ‘Yan Nijeriya Kan Shirin Zanga-zanga
- Tinubu da iyalinsa na neman kassara Nijeriya — Atiku
A cewarsa, ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa guda uku a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar na PDP, Peter Obi na LP da kuma Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar NNPP za su ajiye muradun kashin kansu a gefe, su kulla wata babbar kawance domin kayar da jam’iyya mai mulki ta APC a 2027 tare da ceto ‘yan Nijeriya daga yunwa.
Ya ce da a ce shugabannin jam’iyyar da suka gabata sun yi kokari wajen magance bambance-bambance da rigingimun jam’iyya da kyau, manyan jiga-jigai kamar tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, Kwankwaso da Obi za su kasance cikakkun ‘ya’ya jam’iyyar PDP, kuma da jam’iyyar ta doke Bola Tinubu na jam’iyyar APC a zaben da ya gabata.
“Mun rasa Kwankwaso, mun rasa Peter Obi, inda dukkan wadannan mutane suna cikin jam’iyyar, da mun ci zabe.
“Wannan APC ta ce sun kayar da mu da kuri’u miliyan daya da dori, daya daga cikin wadannan sunaye da na ambata da zai cike mana wannan gibin, kuma da a yau muke kan karagar mulki, kuma tabbas da ‘yan Nijeriya ba za su fuskanci wannan bala’i da suke ciki a halin yanzu ba,” in ji shi.