Jam’iyyar NNPP ta lashe dukkanin kujerun ciyamwn da kansiloli a zaben kananan hukumomi da aka kammala a Jihar Kano.
Jam’iyyar ta lashe dukkanin kananan hukumomi 44 na jihar, kamar yadda shugaban hukumar zabe ta Kano (KANSIEC), Sani Malumfashi, ya bayyana.
- Sin Ta Fitar Da Karfe Tan Miliyan 80.71 A Rubu’i 3 Na Farkon Bana
- MDD Ta Yi Alkawarin Taimaka Wa Nijeriya Wajen Cimma Muradunta Mai Dorewa
Jam’iyyun siyasa guda shida ne suka shiga zaben, wanda aka gudanar cikin lumana ba tare da samun magudi ba.
Ya yaba yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, inda ya bayyana cewa hakan wata alama ce mai kyau ga tsarin zabe a jihar.
An gudanar da zaben ne bayan kotu ta yi fatali da kokarin wasu jam’iyyun siyasa na hana zaben.
A ranar Juma’a, Babbar Kotun Jihar Kano ta bayar da umarnin gudanar da zaben kananan hukumomi, tare da hana duk wani yunkuri nahana zaben.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp