Jama’a barkanku da kasancewa tare da shafin Taskira, shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da yadda rayuwar matasa take tafiya a yanzu, musamman idan muka yi duba da yadda tarbiyyar ‘ya’ya mata ke kara tabarbarewa wanda har a kan rasa gane daga ina matsalar take?.
- Kungiyar Masu Masana’antu Ta Samu Bashin Naira Biliyan 75 Daga Bankin BOI
- Daukakar Nasaba Da Girman Garinsa (SAW)
Dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin TASKIRA game da wannan batun; “Ko me yake janyo tabarbarewar tarbiyar matasa musamman yadda wasu suke mayar da tsiraicinsu tamkar ba komai ba?, Shin laifin waye?, Wadanne irin matsaloli ne ka iya faruwa bayan afkuwar hakan, kuma ta wacce hanya za a gyara?”.
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Comr. Ibrahim Lawan Stk, Sule Tankarkar Jihar Jigawa:
Akwai abubuwa da dama wanda suke lalata tarbiyya har suke haifar da fitar tsiraici wadannan abubuwa sun hada da rashin tarbiyya, koyi da al’adu mararsa kyau, koyi da mutanen banza, kallon fina-finan banza, amfani da wayar salula ta hanyar amfani da kafafafen sada zumunta, rashin jin tsoron Allah, ta’ammali da abokan banza, rashin kulawar manyan mutane masu karfin ikon fada aji a cikin al’umma, laifin malaman addini dama shuwagabbani, talauci, tare da son abin duniya hadi da rashin kula da tarbiyyar yara daga wajen iyaye. Kusan kowa nada laifi akan wannan al’amari duba da yadda idan muka kalli abuwan dake haifar da hankan sai dai babban laifin ya ta’allaka ne ga iyaye sakamakon rashin kulawar su tare da bada tarbiyya ta gari ga yaransu musamman a wannan yanayi da kuma halin da ake ciki a kasar nan. Matsaloli da dama na iya faruwa bayan faruwar wannan al’amari wanda suka hada; shi ga cikin yanayin fargaba tare da damuwa wanda hakan ke taba jin matsayin mutum a matsayinsa na dan’adam, sannan hakan na haifar da matsalar rashin yadda daga wajen iyaye, abokan zama, dama sauran mutane a cikin gari, hakazalika, hanyoyin da za a bi domin yin gyara akan wadannan al’amari ya hada da kula da tarbiyyar tare da sa’idon iyaye akansu, koyawa samari al’adun hausa masu kyau tare da koyi da addinin musulunci, kaucewa aikata abubuwan da mutanen banza ke aikatawa ko koyi dashi, hana samari da matasa kallon finafinan banza, kula da yadda suke amfanin da wayoyinsu musamman a kafafen sada zumunta, kula da abokai wanda suke mu’amala dasu, sa’ido ga matasa da samari musamman daga gurin manyan gari da masu fada aji, fadakarwa daga malam addini akan tarbiyya tare da nasiha domin jin tsoron Allah, taimakon shuwagabbani domin kirkirar dokar yin amfani da waya musamman wajen kalle-kalle tare da amfani da waya wajen yin amfanin da kafofin sada zumunta, samar da aikin yi taimakon daga gwabnati domin yaye talauci musamman a yanayin da ake ciki a yanzu duk na daya daga cikin abubuwan da ka iya kawo gyara akan wannan al’amari. Iyaye sune tushe wajen tabbatar tare da inganta tarbiyyar ‘ya’yansu wanda hakan tasa ya zama wajibi su kasance masu sa’ido akan tarbiyya yayansu da kuma yi musu nasiha akan wanda ya kamata ya zama aboki ko kawa a gare su. ‘Ya’ya ya kamata su kasance masu yin hattara wajen yin abota da dangantaka dasu, tare da kaucewa abin da ka iya taba musu rayuwar su, gwabnati ya kamata ta kirkiro doka akan hakan domin tabbatar da tarbiyyar yara masu tasowa tare da karesu daga fadawa cikin halin da bai kamata su tsinci kansu ba, malamai kuma ya kamata su kasance masu fadakarwa tare da koyarwa a bisa tafarkin addini gamai da illolin tabarbarewar tarbiyya tare da fitar da tsiraici ga al’umma.
Sunana Hafsat Sa’eed Daga Jihar Neja:
Abin da yake janyo tabarbarewar tarbiyya ba komai ba ne face yanayi da ake ciki na talauci, wasu iyayen ba sa iya jurewa za su bar ‘ya’ya su sake su je su yi ta abubuwa a social media wanda bai kamata ba. Wasu kuma ba a san ransu ba iyaye ba sa sani suke yin irin wannan abubuwan, a kashi casa’in dai a halin yanzu wasu iyaye suna sane, dan ni ma akwai ire-iren wasu dana sani hakan ya faru ga yara ne, dana bunciki iyayen sai suka rika nunan ba daga nan ba ne suna sane, kin ga dole zan iya cewa wasu iyayen ne saboda su samo su basu su ci a halin da ake ciki a yanzu. Wasu kuma ba a san ran iyaye ba ne sai dai ba yadda ka iya da ‘ya’ya ka basu tarbiyya daidai gwargwado amma akwai jarabta a cikin rayuwa wanda wani lokacin sai Allah ya jarabce ka a cikin ‘ya’ya to, akwai su kashi daban-daban. Matsalolin da ka iya faruwa yana sakawa yarinya ta rasa mijin aure ko kuma ‘ya’ya a nan gaba idan ka haifi ‘ya’ya za a iya zuwa ana tariyo musu tunda abu na harkar media abu baya taba goguwa in kai ka goge to, yana wajen wani in ya kai shekara goma za a iya tariyo shi a zo a nunawa mutane. Hanya mafi sauki wajen gyara shi ne malamai su duba su yi ta addu’a.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To hakika karancin tarbiyyar addini ce ke yawan jawo wannan matsalar wadda take neman zama ruwan dare a tsakanin matasa a yau, a wasu lokutan ma a iya cewa rashin tarbiyyar addini ce ma ke jawowa daga yaran har iyayen su, domin idan mutum yana da tarbiyyar addini to, zai yi kokari sosai wajen ganin ya bawa ‘ya’yansa irin tarbiyyar daya ke da ita. To magana ta gaskiya masu laifi da farko sune; iyaye domin sune hakkin kula da tarbiyya ya rataya a wuyan su, domin duk wanda zai yi kokari wajen bada tarbiyya to, iyaye yake taimakawa domin sune ke da kaso mafi yawa wajen kula da tarbiyya.Gwamnati ma nada laifi domin ita take da doka a hannunta wanda idan ta ga dama za ta yi amfani da doka wajen ladaftar da duk wani mai kunnen kashi. To na farko dai an sabawa ubangiji kuma za a iya haduwa da fushinsa, sannan kuma akwai zubar mutunci a idon al’umma gashi kuma mutum ya bar tarihin da ‘ya’yansa ba
za su yi alfahari da shi har abada. To shawara ta a nan ita ce ya kamata iyaye su tashi tsaye wajen kula da tarbiyyar ‘ya’yansu domin amana ce Allah ya basu wanda dole ne su yi bayani a kan ta ranar alkiyama.