Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce jam’iyyar NNPP ta mutu kuma za a shafe ta nan ba da jimawa ba.
Da yake jawabi a ranar Talata a Abuja yayin da ya karɓi shugabanni da mambobin Tinubu Support Group (TSG), Ganduje ya bayyana cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a NNPP a 2023, yana shirin komawa APC, jam’iyyar da ya fito daga cikinta.
- Za A Watsa Shirin Bidiyon “Bayanan Magabata Dake Jan Hankalin Xi Jinping” Na Harshen Malay
- Minista Ya Gargaɗi Jami’an Gwamnati Kan Rashin Sanin Ilimin Tantance Ingantattun Labarai
Ganduje ya ce APC a shirye ta ke ta karɓi Kwankwaso da sauran shugabannin jam’iyyun adawa, inda ya bayyana cewa sanannun ’yan siyasa da ’yan majalisa da dama sun fara shigowa APC saboda taɓarɓarewa jam’iyyun adawa, musamman NNPP.
Ya ce: “NNPP ta mutu. Abin da ya rage kawai shi ne a birne ta. Ko Kwankwaso da ya bar jam’iyyar yanzu yana son dawowa. Za mu karɓe shi domin gida zai daqo.”
Ganduje ya ƙara da cewa ƙoƙarin jam’iyyun adawa na yin haɗaka domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu kafin zaɓen 2027 ba zai yi nasara ba.
A gefe guda kuma, Ganduje ya kafa kwamiti sulhu guda uku don sulhunta rikicin APC a Anambra kafin zaɓen gwamna da za a yi ranar 8 ga watan Nuwamba.
Kowanne yankin sanatan jihar — Arewa, Kudu da Tsakiya — yana da mambobi shida da za su yi aiki don haɗa kan ’yan jam’iyyar domin samun nasara a zaɓen.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp