Biyo bayan hukuncin da babbar kotun tarayya da ke da zamanta a jihar Kaduna ta yanke na aminta da sunan Sanata Uba Sani a matsayin dan takarar gwamna a jamiyyar APC da kuma sauran ‘yan takarar 34 na mazabun, dan takarar gwamna a jamiyyar NNPP Sanata Suleiman Hunkuyi da kuma jamiyyar sun ce za su kalubalanci wannan hukuncin.
Hunkuyi da kuma NNPP ne suka shigar da hukumar INEC kara bisa sanya sunan dan takarar gwamna na jamiyyar APC Sanata Uba Sani a matsayin dan takarar APC da kuma sauran ‘yan takarar 34 na mazabun.
A cikin takardar karar da NNPP da Hukunyi shuka shigar a gaban kotun, sun ce, APC ba ta gudanar da sahihin taron ta mazaba ba da ya fitar da daliget din da suka yi zaben fidda gwani ba, wanda kuma har aka fitar da dan takarar gwamna a APC da kuma sauran ‘yan takarar mukaman majalisar dokokin jihar duk na APC, inda a saboda haka, suka bukaci INEC kar ta sa sunayen su a matsayin ‘yan takara a zaben 2023.
Hunkuyi a taron manema labarai a Kaduna ya ce, NNPP ba wai ta kai karar APC ko ‘yan takarar ta ba ne, amma hukumar INEC ta shigar a gaban kotun akan sanya sunan Uba da sauran ‘yan takarar 34.
Ya yi nuni da cewa, a mulkin demokiradiyya ana so ne a yi adalci da kuma gudanar da sahihin zabe, inda ya ya kara da cewa, jamiyyar NNPP ta dogara ne da sashe na 29 da ke a cikin cikin dokar zabe da aka sabunta wacce ta yi bayani karara cewa, daukacin jamiyyun dole ne su mika sunayen ‘yan takarar su da suka shiga aka fafata da su a zaben fidda gwani.