A makwannin da suka gabata, yankuna da dama na kasar nan, sun samu ruwan sama kamar da bakin kwarya. Hukumar kula da yanayi ta kasa (NiMet), a ranar 4 ga watan Fabrairun 2025, ta kaddamar da kundin hasashe kan yadda yanayi zai kasance a kakar noman shekarar 2025.
Kundin ya yi hasashen cewa, za a samu ruwan sama kamar da bakin kwarya a wannan shekara da muke ciki (bana), wanda ruwan saman, mai yiwuwa zai sauka da wuri a shekarar 2025 din.
Tuni dai, kamar yadda dai aka saba, wasu manoma a kasar duk da cewa, daminar kakar 2025 din ba ta riga ta kankama ba, suka fara yin shuka a gonakinsu.
- Radda Ya Raba Wa Manoma Taki A Jihar Katsina
- Sabbin Fasahohin Noma Na Zamani Na Ci Gaba Da Bayyana A Kasar Sin
Misali, rahotannin sun bayyana cewa, a Kananan Hukumomin Akwanga, Lafia da Doma da ke Jihar Nasarawa, sun shuka Irin gyada kawai domin sa ran samun ruwan sama a makon da ya gabata, wanda hakan ya sanya yanzu suke jin tsoro ganin cewa, ba a sake yin wani ruwan saman ba, hakan ya kuma sanya Irin gyadar da suka shuka, zafin rana ya fara lalata shi.
Haka nan ma, batun yake a babban birnin tarayyar Abuja, kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana, musamman ga wasu manoman da ke zaune a wasu sassa na Bwari da kuma wasu kauyuka da ke makwabtaka da Jihar Neja, da suka yi hanzarin yin shuka, su ma suka shiga cikin fargaba ta rashin samun sake saukar ruwan na sama.
Bugu da kari, wasu kwararru a fannin aikin noma, su ma tuni suka gargadi manoman kan kaucewa yin shuka da wuri, inda suka shawarce su da su tabbatar da sun kiyaye da hasashen na hukumar ta NiMet, domin kaucewa tabka asara da kuma yin da-na-sani.
Lokacin Da Ya Fi Dacewa Manona Su Yi Shuka:
Wata kungiya mai bayar da agajin gaggawa, (Christian Aids) tare da hadaka da wasu abokan hudda, sun samar da wata taswira da ke kunshe da lokacin da ya fi dacewa manoman da ke jihohin kasar 36 ciki har da babban birnin tarayayyar Abuja, su yi shuka.
Taswirar wadda ta kasance mai saukin amfanai, sun tsara matakan da suka kamata manoman su bi, na kiyaye lokacin yin shuka, mussamman domin manoman su kauce wa fadawa cikin matsalar irin yadda suka tsinci kansu a ciki a kakar noman shekarar 2024.
Idan za a iya tunawa, hukumar ta NiMet, a wasu bayanai da ta wallafa na farko da suka kuma karade shafukan sada zumunta na zamani a 2025, ta sanar da manoman kasar, ranakun da ya kamata su fara yin shuka da kuma Irin da ya kamata su shuka.
Kazalika, hukumar ta kuma shawarci manoman da su gujewa yin shuka da wuri, duba da bayanan sauyin yanayi da hukumar ta yi hasashen za a iya samu a kasar.
Idan za a iya tunawa, a kakar noma ta shekarar 2024, wasu manoman kasar da dama da suka yi shuka da wuri, sun tabka mummunar asara.
Wani malamain gona mai suna Jacob Auta, ya shawarci manoman kasar cewa; kada su yi saurin yin shuka, inda ya kara da cewa; duba da yadda Irin noma ya yi tsada, ya zama wajibi manoman su sanya ido kafin su fara yin shuka.
Ya yi nuni da cewa, wasu daga cikin Irin noman, ba sa iya jurewa yanayi kamar na zafi, idan an shuka su.
Jacob ya kara da cewa, idan har manoman sun yi shuka kuma ya kasance an kai sama da mako daya ba a samu ruwan sama ba, za su iya tafka asara.
“Haka nan, batun yake a kan sauran amfanin gona, sai dai kawai idan manomi, yana da kayan ban ruwan da zai iya rika yi wa gonarsa ban ruwa,” in ji Jacob.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp