A yayin da daminar bana ta fara kankama a wasu jihohin kasar nan, hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa a kan manoma sai kara kamari yake yi inda hakan ke janyo karin asarar rayukann manoman.
Masu bibiyar al’amura a kasar nan, sun bayyana cewa, kisan da ‘yan bindiga ke yi wa manoma ya yi kamari ne daga zamanin tsohuwar Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, kuma ko da aka rantsar da sabuwar gwamnati, ‘yan bindigar sun ci gaba da cin karen su babu babbaka duk da nasarorin da mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaron kasa, Malam Nuhu Ribadu ya ce jami’an tsaro suna samu a kansu.
- Za A Bude Shafin Karbar Bashin Dalibai A Ranar 24 Ga Mayu
- Shugabannin Sin Da Rasha Sun Tattauna Da Juna
Rahotanin sun bayyana cewa, wannan lamarin ya janyo wasu manoman yin watsi da gonakinsu musamman a jihohin da hare-haren na ‘yan bindiga ya fi kamari a kamar su Zamfara, Benuwai, Sakkkwato, Neja, Filato, Kaduna da kuma Katsina.
Bugu da kari, a wasu jihohin kamar Zamfara, Neja, Kaduna Sokoto, an jima ana zargin ‘yan bindigar da sanya wa manoman haraji kafin su ba su damar noma gonakinsu ko kuma girbe amfanin da suka noma.
An ruwaito shugaban kungiyar manoma ta kasa (AFAN) na Jihar Sokoto, Jamilu Sanusi, yana bayyana cewa, ’yan kungiyarsu sun yi asarar fiye da Naira biliyan 3 wajen biyan kudin fansa ga ‘yan bindiga.
Ya kara da cewa, sama da kashi 80 na ‘yan gudun hijira da ke zaune a sansanin ‘yan gudun hijira daban-daban a jihar manoma ne.
A cewarsa, kasa da kadada 10,000 a jihar manoma suka gaza nomawa a kusan sama da shekaru uku, inda kuma ‘yan bindiga suka hallaka sama da manoma 28 a cikin wannan shekarar a jihar.
A wani ra’ayi da Jaridar Punch ta wallafa a ranar 25 ga Maris, 2024, cikin wata uku daga farkon shekarar nan kawai, kimain manoma 165 ne ‘yan bindiga suka hallaka har lahira. Al’amarin bai tsaya nan ba domin ko a makon da ya gabata, akalla manoma 30 ciki har da wani malamin addini aka yi wa kisan gilla a Jihar Zamfara.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar, ASP Yazid Abu Abubakar, ya tabbatar da aukuwar wannan kisan a kananan hukumomi biyu na jihar.
Kafafen yada labarai sun ruwaito cewa, harin ya auku ne a kananan hukumomin Maradun da Tsafe a yayin da manoman ke aikin sharar gonakansu.
Masana sun yi nuni da cewa, hauhawan farashin kayan abinci a daukacin fadin Nijeriya na da nasaba da ta’asar da ‘yan bindiga ke ci gaba da yi.
Wasu alkaluma sun bayyana cewa, hauhawan farashin kayan abinci a watan Maris, 2024, ya kai kashi 40 a cikin dari, inda ya rika karuwa tun daga na watan Janairun 2024 wanda yake kashi 35.41 a cikin dari
A kwanan baya, an ruwaito shugaban Karamar Hukumar Agatu da ke Benuwe, Yakubu Ochepo yana tabbatar da wani harin da ‘yan bindigar suka kai a a yankin Ogbaulu inda suka yi wa manoma uku yankan Rago a cikin gonakansu.
Kazalika, an ruwaito wani shugaban kungiyar manoma a Jihar Nasarawa Mista Denis Utsa, yana tabbatar da kisan wasu manoma uku a yankin Kadarko da ke a Karamar Hukumar Keana ta jihar, tare da kuma hallaka wasu manoma uku a yankin Tse-Abir Azer da ke a Kadarko.
A karamar hukumar Bokkos ta Jihar Filato an ruwaito wani manomi mai suna Stephen Garuba yana cewa, bai san adadin manoman da ‘yan bindiga suka sace ba, inda ya ce, sun kuma kona amfanin gona na miliyoyin Naira.
A cewarsa, hare-haren na ‘yan bindigar ya fi kamari a Kanannan Hukumomin Munya, Shiroro, Meriga, Paikoro, Rafi Mashegu, Wushishi da Borgu.
A Jihar Borno, nan ma abin bai sauya zani ba, sai dai, babu wanda zai iya fadar adadin manoman da ‘yan bindiga duka kashe.
Bugu da kari, a Jihar Kaduna, manoma nusamman na Shinkafa a jihar na ci gaba da kokawa kan hare-haren da ‘yan bindiga ke kai masu wanda haka ya dakatar da su zuwa gonakansu don nomawa.
An ruwaito shugaban kunkiyar, Alhaji Mohammed Umar Numbu yana bayyana cewa, kimanin ‘ya’yan kungiyar 72,000 a yanzu, ba sa iya zuwa gonakansu.
Sakamakon ta’asar da ‘yan ta’addan ke tafkwa, ‘Yan Nijeria na ci gaba da rayuwa cikin mawuyacin hali. Inda sabbin rahotannin da ke fitowa ke nunar da cewa manoma na barin gonakinsu a jihohi da dama saboda ta’addanci da sauran nau’o’in rashin tsaro.
A cikin wani rahoto da aka fitar ranar 20 ga Maris, Rundunar Sojan Nijerriya ta bayyana cewa manoma suna mutuwa a sababin hare-haren ‘yan ta’addan daji. Wasu kuma ana garkuwa da su. Jihohin da suka fi fama da wannan lamari sun hada da Binuwe, Sokoto, Neja, Pilato. Kaduna, Zamfara, da Katsina.
Ba abin mamaki ba ne yadda tsadar kayan abinci ke kara ta’azzara a fadin kasar nan, yayin da manoma ke watsi da sana’ar da suka gada iyaye da kakanni saboda tashe-tashen hankula.
Ana ci gaba da kiraye-kiraye ga Gwamnatin Bola Tinubu da ta kawo karshen kashe-kashen da ake yi wa manoma a fadin kasar nan, ta hanyar daukar kwararan matakai na sabunta tsaro.
Baya ga manoma 165 da aka ruwaito sun rasa rayukansu a zuwa Maris, 2024. A Benuwai, ‘yan bindiga sun yi wa manoma 15 kisan gilla a Karamar Hukumar Apa inda hakan ya kara adadin wadanda aka kashe a yankunan jihar zuwa 130. Hakazalika, kashe-kashen manoman a Sakkwato, ya yi sanadin mutuwar 28, in ji kungiyar manoman Nijeriya. Haka nan ta ce ‘yan bindigar sun kori manoma a Neja da Filato.
Wata sanarwa da wata kungiyar tattara bayanan sirri ta SBM ta fitar a watan Maris, ta ce ana garkuwa da ‘yan Nijeriya biyar a kullum a shekarar 2024. ‘Yan bindiga suna garkuwa da daruruwan mutane musamman a jihohin Kaduna, Sokoto da Borno, in ji ta.
Bayan kisan da ‘yan ta’addan ke wa manoma a farkon damina, har ila yau kalilan da suka samu dama suka noma dan abin da za su ci, su ma ba su tsira ba domin ‘yan ta’addan sukan sanya haraji ga manoman kafin su kyale su, su girbe amfanin gonakinsu musamman a sassan jihohin Neja da Kaduna, lamarin da ya tilasta wa manoma zama a gida cikin yunwa da rashin taimako.
Gwamnatin Tinubu dai ta yi alkawarin tabbatar da aikin gona na rani da damina ta hanyar ware makudan kudade daban-daban ciki har da na noman masara akalla na Naira Biliyan 200, bayan cire tallafin mai, sai dai har yanzu babu wani abin a zo a gani kan hakan.