Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Ƙasa NPA ta bayyana cewa, an yi wa tsarin amfani da na’urar da ake kira a turance ta Electronic Call-Up system, garanbawul wanda ta ce, za a fara gudanar da ayyuka da ita, a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa Port .
Manajan Tashar ta Apapa Mista, Debo Lawal us bayyana hakan a hirar da da manoma labarai rai, a ranar Litinin da ta wuce, a jihar Legas
Lawal ya sanar da cewa, ɗaukacin tsarin na ETO, an yi masa garanbawul gaba ɗayansa musamman domin ya kai matki irin na duniya da ake amfani da shi.
- Yadda Tashar Jirgen Ruwan Apapa-Moniya Za Ta Taimaka Wa Masu Safarar Fitar Da Kaya
- NPA Za Ta Sauya Mazaunin Na’urar Tantance Jiragen Ruwa Da Ke Apapa
Ya bayyana cewa, kamar yadda a baya, manyan moto in da ke bin hanyoyin na cikin Tashar ta Apapa saboda rashin samar da shingaye, wanda hakan ke haifar da cinkoson motocin, amma bisa yin wannan garanbawul ɗin, waɗannan matsalolin, za su zama tarihi a Tashar ta Apapa.
Ya ci gaba da cewa, wannan garanbawul ɗin, za ta tabbatar da ana bin doka da oda tare da kuma tabbatar da kowacce babbar mota, na bin ƙa’idojin da aka shinfiɗa.
Lawal ya ƙara da cewa, ɗaukacin guraren da Jiragen Ruwa ke tsaya, akwai launin da kuma lamba da aka amince,manyan motocin za su rinƙa yin amfani da su, domin yin zirga-zirga a Tashar ta Apapa.
“Misali, a APMT, manyan motocin za su rinƙa yin amfani da lamba 001 mai ɗauke launin ruwan bula, inda kuma a ENL Consortium, za su rinƙa yin amfani da lambApapaETO bisa nufin rage cunkoso a ciki da kuma wajen Tashar ta Apapa.ɗauke da launin rawaya,” Inji Lawal.
Ya bayyana cewa, wannan sabon garanbawul ɗin da aka yi, za ta taimaka wajen matsalar ƙetarawa hanyar da manyan motocin ke fuskanta a Tashar ta Apapa.
Lawal ya ci gaba da cewa, bisa nazarin da aka gudanar a Tashar ta Apapa, an gano cewa, manyan motocin a Tashar da ke yin amfani da ENL guda 100 a kullum ke shiga tashar waɗanda kuma ba dukkanin su ne ake da buƙatar su yi amfani da hanyoyin ba,
Ya jaddada cewa daga yanzu duk manyan motocin da za su rinƙa shiga cikin Tashar ta Apapa dole ne sai rinƙa samun amincewar gwamnati.
Idan za a iya tunawa, Hukumar ta NPA, a shekarar 2024 ne, ta ƙaddamar da tsarin na ETO bisa nufin rage cunkoso s ciki da kuma wajen Tashar ta Apapa tare da kuma samar da dauƙin gudanar da ayyukan kasuwanci a Tashar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp