Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, ta kara wa’adin dakatar da kudin da take caza kan kayan da Jiragen Ruwa suka shiga da su zuwa cikin Tashoshin Jiragen Ruwan da kuma kudin ajiyar kayan a Tashoshin zuwa Kwanuka 14.
NPA ta dauki wannan matakin ne,bayan karewar ainahin wa’adin dakatarwar da ta yi a baya na Kwanuka 21.
- Ba Sulhu Ko Sassauci Ga Ƴan Bindiga A Zamfara – Gwamna Lawal Dare
- Salon Zamanantarwa Na Sin Kyakkyawan Misali Ne Ga Kasashen Afirka
Idan za a iya tunawa. a ranar 24 ga watan Maris na shekarar 2020 ne Hukumar ta NPA ta sanar da dakatar da karbar wadannan kudaden biyo bayan bullar annobar Korona a kasar nan.
Sai dai ,duk da wannan umarnin masu kula da shigo da kaya da sauransu a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar, sun ci gaba da karbar wadannan kudaden wanda hakan ya sanya wasu abokan hada-hadar kasuwanni a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar, suka yi barazanar kai kara a gaban kotu.
Kazalika, a ranar Alhamus da ta gabata kungiyar ta a bukaci ‘ya’yanta da su tabbar da suna ajiye da rasidan shigar kudaden da suka biya na cazar kudaden ajiye kayan da suka yi a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar wanda hakan zai ba su damar karbar kudaden su, da suka biya a nan gaba.
Amana a cikin sanarwar da Hukumar ta NPA ta fitar mai taken daukar matakai ga masu amfani da Tashoshin Jiragen Ruwan kasar biyo bayan bullar annobar Korona wadda kuma Janar Manaja na sashen Kula da walwalar jama’a da dabarun samar da bayanai na Hukumar ta NPA Jatto Adams ya fitar ta umarci daukacin masu Kula da harkokin Hukumar da su dakatar da cazar duk wasu kudaden na shigo da kayan zuwa cikin Tashoshin Jiragen Ruwan kasar har zuwa wasu Kwanuka 14.
Wannan umarnin ya biyo bayan umarnin da tsohuwar gwamatin marigayi Shugaban kasa Muhammad Buhari ta yi ne bayan bullar annobar Korona a na fadadar da aka yi ne, bayan bullar annobar Korona a ranar 12 ga watan Afirilun shekarar 2020, ” A cawar sanarwar .
Sai dai, Hukumar ta jaddada cewa, ba za ta lamunci kin yin biyayya da wannan umarnin da ta bayar ba kuma ba za ta yi wani sako-sakon daukar matakai ga duk wanda ya sabawa wannan umarnin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp