Hukumar kula da tashoshin Jiragen Ruwa ta kasa NPA, ta sanar da gudunmawar da za ta bayar wajen wanzar da umarnin gwamnatin tarayya a fanin sanya ido na gudanar da aikace-aikace.
Kazalika, ta bayyana rawar da za ta taka, wajen kara tabbatar da tsaro tare da sauran masu ruwa tsaki, domin a tabbatar samun cin nasara a shirin sayar da danyen mai da sauran dangoginsa, a kan farashin Naira ga matatar mai ta Dangote.
- GORON JUMA’A
- Hadarin Kwale-kwale A Kaiama: Gwamnan Jihar Kwara Ya Bayar Da Tallafin Naira Miliyan 100
Ta sanar da hakan ne, a cikin sanarwar da Manajin Darakta na hukumar Dakta Abubakar Dantsoho ya fitar.
Dantsoho ya ce, kwamitin wanda ya kasance a karkashin kulawar hukumar, zai sanya ido wajen ganin cewa, ana sayar da danyen man a kan farashin Naira.
Manajin Daraktan ya bayyana haka ne a jawabinsa a wata ganawa da aka gudanar a jihar Legas, inda ya bayyana jin dadinsa a kan hobbasan da hukumar ke ci gaba da yi don ta sauke nayin da aka dora mata.
Dantsoho ya ci gaba da cewa, aikin ya hada da; wasu wakilai na hukumar, jami’an rundunar sojin ruwa, jami’ai daga kamfanin NNPCL da na kamfanin rukunonin Dangote.
Sauran ya ce, sun hada da; jami’an hukumar tattara haraji na kasa FIRS da na hukumar NMASA da kuma na hukumar NDLEA.
An kuma nada babbar jami’a a sashen ayyuka a hukumar NPA Madam Maureen Ogbonna, a matsayin mai kula da sashen OSS.
Kazalika, jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, karamin kwamiti na kula da sayar Danyen man a kan Naira, ya tabbatar cewa, NNPC ya tura danyen man zuwa ga matatar man Dangote, wanda aka sayar wa da kamfanin a kan Naira, a ranar daya ga watan Okutobar 2024.
Bugu da kari, a ranar 13 ga watan Satumbar 2024, kwamitin ya sanar da cewa, a zaman da majalisar zartarwa da shugaba Bola Tinubu ya jagoranta, ta amince da sayar da danyen mai da sauran dangoginsa ga matatun mai na cikin gida Nijeriya, a kan farashin Naira.
Kwamitin ya sanar da cewa, daga ranar daya ga watan Okutobar 2024, NNPC ya fara tura gangunan danyen mai ga matatar mai ta Dangote da suka kai akalla 385,000 a duk rana daya, wadanda kuma za a biya kudinsu, a kan farashin Naira.