Hukumar gudanarwar gasar Firimiyar Nijeriya, ta ci tarar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Naira miliyan biyu saboda rashin da’a bayan ta sha kashi da ci daya mai ban haushi a hannun Nasarawa United a gasar NPFL.
A yayin wasan, kwallon da aka zura wa Pillars ta haifar da takaddama, wanda ta kai ga kyaftin kungiyar, Ahmed Musa, soki alkalin wasan.
Haka kuma, an dakatar da dan wasan Pillars Ugochukwu Gabriel daga buga wasanni tara saboda nuna rashin da’a.
NPFL ta gargadi Pillars kan korafin da ta yi a kafafen sada zumunta, inda ta ce kungiyar ta kara yin haka za ta mata hukunci mai tsanani.
Haka kuma, NPFL ta gargadi Kano Pillars game da yin tsokaci a bainar jama’a, inda aka bukace su suyi amfani da hanyoyin da hukumar ta tanada wajen bayyana korafe-korafensu.
Kungiyar na da damar daukaka kara cikin sa’o’i 48.