Hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) a birnin tarayya Abuja, ta bankado wani yunkurin kaddamar da jerin hare-haren ta’addanci da makayan ISWAP suka kitsa aiwatarwa a Abuja.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da Kwamandan hukumar NSCDC reshen Abuja, Peter Maigari, ya fitar a ranar Juma’a, ya ce, “bayanan sirri da muka tattaro mun gano mambobin ISWAP sun kammala shirinsu na kaddamar da jerin hare-haren a wasu zababbun wurare a cikin birnin tarayya.”
- Harin Kuje: ‘Yan Sanda Sun Cafke Dan Boko Haram Da Ya Tsere A Nasarawa
- Babbar Sallah: Bana Raguna Sun Gagari Kundila
Kwafin sanarwar jan hankali da aka aike da ita ga babban sakataren hukumar kula da birnin tarayya da kuma LEADERSHIP ta ga kwafin, na cewa: “An samu bayanan sirri da ke cewa ISWAP ta dauki alhakin harin gidan yarin Kuje a ranar 5 ga watan Yulin 2022 don fitar da mambobinsu.
“Wannan danyen aikin da suka yi ya basu kwarin guiwar sake shirin harar jama’a da aikace-aikacen ta’addancinsu.”
Sanarwar ta ce, ‘yan ta’addan sun shirya kai hare-haren ne ga cibiyoyin tsaro, makarantu da cocina da wuraren ibada domin aiwatar da aikinsu ga al’umma.
Maigari, daga bisani ya shawarci a sake nazarin dabarun tsaro domin dakile aniyar ‘yan ta’addan.