Kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya (NUJ), reshin Jihar Kebbi ta mika ta’aziyya ga iyalan Ibrahim Musa Argungu, tsohon mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai ga tsohon Gwamnan jihar, Alhaji Saidu Dakingari, wanda ya rasu a daren ranar Litinin.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Alhaji Ahmed Idris, sakataren kungiyar NUJ na jihar, da aka raba wa manema labarai a Birnin Kebbi.
- Hunkuncin Sauke Wa Mamaci Alkur’ani Bayan Ya Mutu
- Kasar Sin Ta Harba Na’urar Kuafu-1 Ta Farko Kan Binciken Hasken Rana
“Cikin alhini, kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya (NUJ) reshen Jihar Kebbi na ta’aziyya ga iyalan Alhaji Ibrahim Musa Argungu, tsohon mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai ga tsohon Gwamna Saidu Dakingari.
“Marigayi Ibrahim Musa Argungu ya yi aiki da Gidan Radiyon Tarayya na Nijeriya (FRCN) Kaduna kafin ya koma Kamfanin Karfe na Ajaokuta.
“Marigayin ya bar mata biyu da ‘ya’ya bakwai kuma an yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a ranar Talata a Jihar Kaduna,” inji shi.