Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau cewa, bunkasuwar kasar Sin bunkasuwa ce ta bangaren dake son zaman lafiya a duniya, wadda ta samar da karfi da damammaki ga bunkasuwar duniya. Nuna bambanci ga Sin da hana hada kai da Sin, ba su dace da moriyar kowane bangaren duniya ba.
Mao Ning ta bayyana haka ne yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa, lokacin da take karin haske game da kalaman shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz kan kasar Sin.
A kwanakin baya, shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz ya rubuta sharhi a mujallar harkokin waje, inda ya yi nuni da cewa, bai kamata bunkasuwar Sin ta zama dalilin nuna mata bambanci ba, kana bai kamata a kayyade hadin gwiwa tare da kasar Sin ba.
Mao Ning ta bayyana cewa, Sin ta tsaya tsayin daka kan manufofin harkokin waje na tabbatar da zaman lafiya da samun bunkasuwa tare a duniya, kana ta yi kokari wajen sada zumunta da hadin gwiwa tare da ragowar kasa da kasa. A halin yanzu, an shiga lokacin raya tattalin arziki bisa tsarin bai daya a duniya, da samun moriyar juna. Sin ta riga ta hade da duniya a fannin tattalin arziki da tsarin kasa da kasa, kuma duniya ba za ta koma baya zuwa yanayin rarrabuwa da rufe kofa ba. Babu kasar da za ta iya rayuwa ita kadai da ma rufe kofa, nuna bambanci ga juna zai kawo illa ga moriyar kowa da kowa. (Zainab)