Darwin Nunez ya shigo daga baya ya zura kwallaye biyu yayin da Liverpool ta doke Newcastle United da ci 2-1 a gasar Premier ranar Lahadi.
Hakan ya biyo bayan jan kati kai tsaye da suka samu bayan dawowa hutun rabin lokaci na kyaftin din Virgil van Dijk.
- Liverpool Ta Shiga Cikin Masu Neman Sofyan Amrabat
- UEFA Za Ta Biya Magoya Bayan Liverpool Kudin Tikitin Su
Dan wasan na Uruguay din ya zura kwallo a minti na 77 tun bayan zura kwallo a ragar Leeds United a watan Afrilu.
Dan wasan mai shekaru 24 ya nuna yana daga cikin hazikan yan kwallon Liverpool.
An baiwa Van Dijk jan kati bayan dawowa hutun rabin lokaci,Inda alkalin wasa John Brooks ya nuna masa jan kati kai tsaye bayan ya yi wa Alexander Isak keta a gefen fili.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp