An bai wa dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Darwin Nunez jan kati, bayan da suka koma zagaye na biyu a lokacin wasa da kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace a wasan da suka tashi 1-1 a filin wasa na Anfield.
Hakan ya sa sabon dan kwallon da Liverpool ta dauka daga kungiyar kwallon kafa ta Benfica a bana, ba zai buga wa kungiyar wasanni guda uku ba a gasar Premier League ta bana wanda kuma babban kalubale ne ga kungiyar.
Hakan ya biyo bayan jan katin da aka yi masa a wasan farko da ya fara yi a filin wasa na Anfield ranar Litinin din data gabata bayan da dan kwallon tawagar Uruguayan din ya yi wa mai tsaron bayan Palace, Joachim Andersen gware da ka.
Dama dai a makon farko Liverpool ta tashi 2-2 a gidan Fulham, inda Nunez da Mohamed Salah ne suka ci kwallayen kuma kawo yanzu kungiyar ta buga wasanni biyu ba tare da samun nasara ba.
Amma kociyan Liverpool din Jurgen Klopp ya bayyana cewa yana fama da karancin masu cin kwallaye, bayan da Diogo Jota ke jinya, Roberto Firmino bai buga fafatawar da Crystal Palace ba.
Nunez wanda ya ci wa Liverpool kwallo daya a wasan Premier League ta bana, ba zai buga haduwa tsakanin Liverpool da Manchester United ba a ranar Litinin a katafaren filin wasa na Old Trafford.
Kawo yanzu ba’a da tabbaci ko Firminho zai warke kafin litinin domin ya buga wa Liverpool wasan mako na uku sannan wasa na gaba da dan kwallon mai shekara 23 da ba zai buga ba shi ne karawa da Bournemouth a ranar Asabar 27 da wanda Liverpool za ta kece raini da Newcastle United.
A dokar gasar filimiyar Ingila dai yin keta da ganganci kan sa a kara hukuncin zuwa wasa hudu, amma ana sa ran dan kwallon wasa uku ne ba zai buga ba kuma hakan babbar matsala ce ga kungiyar mai neman lashe gasar ta firimiya.