Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, ya bukaci marayun da ke makarantar marayu a garin Maiduguri a Jihar Borno da su dauki iliminsu na zamani da muhimmanci, inda ya ce, ilimin ne kawai zai inganta rayuwarsu.
Obasanjo, ya sanar da hakan a jiya Juma’a a ziyarar da kai a makarantar Islamiya ta Future Prowess, inda ake koyar da daruruwan marayun da ‘yan ta’addar Boko Haram suka kashe iyayensu.
- Gwamna Wike Ya Karyata Batun Maka Atiku Da Tambuwal A Kotu
- Ba Laifi Don Musulmi Sun Yi Murnar Shigar Sabuwar Shekarar Musulunci
Ya ce, yau shekaru uku ke nan da na ziyarci makarantar kuma na lura, ana samun ci gaba a makaratntar, inda ya kara da cewa, daukacinku marayu ne, amma da zarar kun iso nan kun tashi ba a matsayin marayu ba.
Daya daga cikin marayun wanda kuma dalibi ne a makarantar dan shekara 16 mai suna Mustapha Bukar ne ya tarbi Cif Obasanjo a lokacin ziyarar, inda ya nuna wa Obasanjo yadda ‘yan Boko Haram suka hallaka iyayensa a gabansa, inda Obasanjo ya tausaya masa ya kuma danganta abin a matsayin abin tausaya.
Cif Obasanjo ya kuma roki marayun da su yafe wa ‘yan ta’addar da suka kashe Iyayensu, inda ya kara da cewa, idan ku ka yafe masu Allan zai ci gaba da lura da ku.