Kotun koli ta jingine hukuncin karar da jam’iyyar PDP da dan takararta suka shigar kan zaben gwamnan Jihar Ogun da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
A karar, Adebutu na neman a soke nasarar Dapo Abiodun a matsayin wanda ya lashe zaben.
- Fataucin Yara: ‘Yansanda Sun Ceto Jarirai 3, Sun Cafke Mutane 16 A Gombe
- A Kara Yawan Jami’an Tsaro A Hanyar Abuja- Kaduna – Sufeton ‘Yansanda
Yana kalubalantar sake zaben Abiodun ne bisa hujjar cewa ba a bi dokar zabe ta 2022 ba, inda ya dogara da cewar an yi cin hanci da rashawa.
A zaman sauraron karar da Adebutu ya shigar, kwamitin mutum biyar na kotun kolin karkashin jagorancin Mai shari’a John Inyang Okoro ya ki sauraron kararrakin da jam’iyyar APC da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) suka shigar.
PDP da Adebutu suna son kotun koli ta yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara da ke Legas ta yanke a ranar 23 ga watan Nuwamba, na tabbatar da nasarar Adiodun.
Idan za a tuna, alkalai biyu na kotun da ke kasa sun yi watsi da karar da Adebutu ya shigar saboda rashin cancantar su.
Sai dai , lauyan wadanda suka shigar da kara, Chris Uche SAN, ya ce kamata ya yi INEC ta sake gudanar da sabon zabe a rumfunan zabe 99.
Ya ce sake ayyana gwamnan da INEC ta yi a matsayin wanda ya lashe zaben ya saba wa doka.
Abiodun Owonikoko, lauyan wanda ake kara, ya bukaci kotun kolin ta yi watsi da daukaka karar.