Sabon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Dani Olmo ya fara wasa da kafar dama a Barcelona, bayan da ya jefa kwallon da ta yi sanadiyar samun nasarar Barcelona akan Rayo Vallecano.
Olmo ya canji Ferran Torres bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, hakan ya canza yanayin wasan Barcelona wanda ta ke neman farke kwallo a lokacin da ya shigo.
- Muhalli Mai Kyau Na Kasar Sin Ya Sake Dawo Da Giwaye
- Tawagar Jami’an Lafiya Ta Kasar Sin: Yabon Gwani Ya Zama Dole
Talla
A minti na 82 Olmo ya yi abinda ya kawo shi Catalonia inda ya takarkare ya tika kwallon da Lamine Yamal ya bashi a ragar Vallecano.
Da haka ne Barcelona ta dare akan teburin gasar Laliga ta bana da maki 9 da kuma kwallaye 3 a raga.
Talla