Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Nuna Damuwa Kan Yawaitar Hare-haren Da Ake Kai Wa Jami’an Soji
Majalisar Dattawan Nijeriya ta bayyana matuƙar damuwa kan tabarbarewar harkokin tsaro a ƙasar, tana mai gargaɗin cewa sacewa da kashe...
Majalisar Dattawan Nijeriya ta bayyana matuƙar damuwa kan tabarbarewar harkokin tsaro a ƙasar, tana mai gargaɗin cewa sacewa da kashe...
Sakatare janar na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar Xi Jinping ya ba da muhimmin...
Ranar 6 ga watan Yuli ita ce ranar raya kauyuka ta duniya. An kafa wannan rana ne saboda kusan kashi...
Gwamnonin da aka zaba a zangon farko na jam’iyyar APC a yanzu haka suna wani taron sirri a Birnin Kebbi,...
An kai kayayyakin taimakon jin kai na gaggawa na farko da gwamnatin Sin ta ba kasar Venezuela zuwa filin jirgin sama na kasa da kasa na Simon Bolivar na birnin Maiquetia da ke kusa da Caracas, babban birnin kasar Venezuela a jiya Litinin. Ministan harkokin waje na Venezuela, Yvan Gil, da jakadan Sin a Venezuela, Lan Hu, sun kasance a filin jirgin don tarbar kayayyakin. Minista Gil ya ce, tun bayan da girgizar kasa mai karfi ta abka wa Venezuela, bangaren Sin yana ta tuntubar gwamnatin Venezuela akai-akai. Ya kara da cewa, wadannan kayayyakin taimakon sun hada da tantuna, janareto da sauransu, kuma suna da matukar muhimmanci ga mutanen da suka rasa gidajensu sakamakon bala’in, tare da nuna dangantakar abokantaka bisa manyan tsre-tsare a ko da yaushe cikin ko wane yanayi da ke tsakanin kasashen biyu, kamar yadda Hausawa ke cewa, Mahdi ka ture. Baya ga haka kuma, ministan ya ci gaba da cewa, bayan aukuwar bala’in, Sinawa mazauna Venezuela da kamfanonin Sin dake kasar sun samar da taimako cikin gaggawa, kana sun shiga aikin ceto tun daga farkon lokacin da abin ya faru, don ba da kulawa ga mutanen da suka rasa matsugunansu, kuma an ga al’amura da dama na kirki masu ratsa zuciya. (Bilkisu Xin)
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce abu ne a fili cewa kayayyaki da...
Bayan shafe tsawon shekaru 105 da kafuwar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin da yadda gwamnati karkashin jam’iyyar ke ci gaba da jagorantar kasar Sin cikin hikima da hangen nesa da tarin nasarori, ba na zaton akwai wani abu da gwamnati za ta bullo da shi, da zai sa a ga baikenta kamar yadda wasu suke yi. Salon shugabanci da nasarorin da kasar Sin ta samu cikin gomman shekaru, ya nuna mana cewa, gwamnatin kasa ce kadai ke da alhakin tafiyar da harkokinta yadda ya dace da yanayi da jama’arta, kuma ita ce ta fi kowa sanin abun da ya dace da al’ummarta. Yadda wasu kasashen yamma da kafafensu na yada labarai ke kokarin jirkitawa da yada jita-jita game da sabuwar dokar kasar Sin dake nufin kara tabbatar da dunkule dukkan kabilun kasar wuri guda, abun mamaki ne matuka. Manufar dokar dai ita ce karfafa hadin kan kasa da tabbatar da daidaito da kuma inganta mu’amala tsakanin kabilu daban-daban. Duk wanda ke bibiya ko ya ziyarta ko yake zaune a kasar Sin kamar ni, to tabbas ya san yadda gwamnatin kasar ke mayar da hankali kan dukkan al’ummominta ba tare da wariya ko son kai ba, don haka me ya sa za ta fitar da dokar da za ta nuna wariya ko musgunawa jama’arta? Daya daga cikin abubuwan da suka haifar da hadin kai da ci gaban al’ummar kasar Sin shi ne, sanin cewa dukkansu Sinawa, ’yan uwan juna, kuma tsintsiya madaurinki daya, kishin kasarsu na gaba da komai. Kuma wannan kishin da suke da shi a zukatansu ne, kashin bayan ci gaban da suke samu a kai a kai kuma na ban mamaki. A tunanina, masu fassara wannan doka ta bahaguwar hanya, na yi ne domin cimma wata manufa tasu, ko kuma son ganin al’ummomin kasar sun fada cikin matsalar rarrabuwar kawuna kamar yadda suke ciki, abun da na yi imanin kasar Sin ba za ta taba bari ba. (Fa’iza Mustapha)
Aƙalla mutane 15 ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a yankin Makabartar Musulmi da ke...
Gwamnatin Sin ta aika da zagayen farko na kayayyakin agajin gaggawa ga Venezuela, domin tallafa wa ayyukan jin kai sanadiyyar...
Hukumar kwallon ta nahiyar Turai (UEFA) ta soki matakin da hukumar kwallon kasa ta Duniya (FIFA) ta dauka na dakatar...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.