A ƙalla dattawa 250 ne a jihar Bauchi suka amfana da tallafin Naira miliyan 50 a ƙarƙashin shirin tallafa wa dattawa na gidauniyar matar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu ‘Renewed Hope Initiative Elderly Support Scheme’ (RHIESS).
Dattawan waɗanda kowanne ya amshi kyautar N200,000 lakadan a yayin ƙaddamar da shirin tallafa wa dattawa karo na uku da ya gudana a ranar Talata a filin wasanni na Dr. Rilwanu Sulaiman Adamu Square, da ke gidan gwamnatin jihar Bauchi, tallafin ya gudana ne a ƙarƙashin shirin gidauniyar na kyautata jin daɗi da walwalar jama’a.
- Shugaba Xi Ya Saurari Rahoton Aiki Daga Kantoman Yankin Musamman Na Hong Kong
- Sin Ta Dauki Matakan Kakkaba Takunkumi Kan Tsohon Shugaban Rukunin Tsaron Kasar Japan
Da ta ke jawabi yayin miƙa kuɗaɗen ga waɗanda suka samu cin gajiya, Ko’odinetan gidauniyar RHI a Arewa Maso Gabas kuma matar gwamnan jihar Bauchi Dr. Aisha Bala Mohammed, ta nanata aniyar Gwamnatin tarayya na ci gaba da kyautata jin daɗi da walwalar dattawan mutane a faɗin ƙasar nan.
A cewarta daga cikin Dattawan da suka amfana da tallafin a Bauchi an haɗa har da tsofaffin sojoji da ‘yansanda, tana mai cewa an yi hakan ne domin agaza musu da nema musu yadda rayuwa za ta ɗan yi musu sauƙi a matsayinsu na dattijai.
Ta ce a kowace jiha daga cikin jihohi 37 ciki har da FCT an zaɓi mutum 250 da za su amfana da wannan tallafin.
Da ta ke samun wakilcin matar mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Asma’u Muhammad Jatau, ta ce, taken tallafin shi ne ‘samar da farin ciki a zukatan dattawa,’ da aka yi da nufin kyautata musu rayuwa da mutuntasu.
A’isha Bala ta kuma yaba wa shugaban gidauniyar RHI, wato Sanata Oluremi Tinubu, bisa ƙoƙarinta na tallafa wa mutane musamman marasa ƙarfi a cikin al’umma.
Wasu da suka ci gajiyar tallafin sun gode wa matar shugaban ƙasa bisa kyautar, inda suka nuna cewa kuɗin zai rage musu raɗadin rayuwa.














