Tsohuwar zakarar tseren mita 100 ta duniya, Tobi Amusan, da mai tseren mita 400, Ezekiel Nathaniel, sun sami nasarar shiga gasar Olympics da za a yi a shekara mai zuwa a birnin Paris na kasar Faransa.
A watan Disambar da ta gabata, hukumar wasannin guje-guje ta Duniya ta bayyana hanyar da za a bi don samun cancantar shiga wasannin motsa jiki a Paris 2024.
- Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Arsenal Da Manchester United
- Kwallon Mata: Ingila Ta Kai Wasan Karshe Bayan Doke Australia
Amusan ta zama ‘yar wasan Najeriya ta farko da ta samu damar shiga gasar ta samu wannan matsayi ne a gasar BAUHAUS-Galan Diamond League da aka yi a birnin Stockholm na kasar Sweden, a ranar 2 ga watan Yuli, inda ta yi gudun dakika 12.52 a gasar tseren mita 100 a gasar Olympiastadion.
An saita ma’aunin shiga gasar mita 100 a dakika 12.77.
Amusan mai shekaru 26 ta kafa tarihin zama ta farko da ta yi gudun fanfalaki na mita 100 a dakika 12.34 a gasar Silesia Kamila Skolimowska Memorial Diamond League a Chorzów, Poland ranar 16 ga Yuli.
Nathaniel, wanda ya rike kambun tseren mita 400 (secs 48.42) a Najeriya, ya samu tikitin shiga gasar Olympics ta farko ta hanyar fafatawa a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya da aka yi a Budapest, kasar Hungary.