Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa, Reno Omokri,ya bukaci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, kar ya kunno wutar rikici da za ta babbake Nijeriya saboda ya fadi zaben shugaban kasa a 2023.
Omokri ya bayyana hakan ne a lokacin wani tattaunawa da gidan talabijin na Channels.
Haka kuma,Omokri ya bukaci a kaddamar da rahoton Uwais kan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
Ya ce, “Akwai bukatar mu yi amfani da rahoton Uwais game da INEC,wanda ya kamata a cire ikon shugaban kasa na nada shugaban INEC da kwamishinonin zabe.
“Hakan zai sa a samu ingantaccen shugabanci a hukumar da kuma zaben Nijeriya. Ina kara so a ci gaba da fadakarwa kan amfani da kayayyakin gida. Ina takaicin yadda fadakarwar da yi sakwa-sakwa lokacin gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu.
“Muna bukatar ci gaba da fadakarwa na sayan kayayyakin Nijeriya a dukkan matakan gwamnati.Akwai bukatar habaka kayayyakin Nijeriya.
“Muna sanar da mutane cewa idan har akwai kayan da aka sarrafa a Nijeriya shi ya kamata a saya fiye da na kasashen waje.Akwai kayayyakin Nijeriya da yawa masu inganci da kamfanin Dangote ke sirrafawa da irinsu Glo da Inmoson da fly Air Peace,”in ji shi.
Idan za a iya tunawa dai, Omokri ya caccaki Obi kan maganarsa na cewa abun kunye ne a ce kasar Ukraine da yaki ya dai-daita ita ke bai wa Nijeriya tallafin abinci.
A ranar Litinin da ta gabata ce, Obi ya ce abun kunya ne Nijeriya ta amshi tallafin kayayyakin abinci daga kasar Ukraine da ke gwabza yaki da Rasha.
Omokri ya ce, “Bai kamata Peter Obi ya ce abun kunya ne ga Nijeriya ta amshi tallafin kayan abinci daga kasar Ukraine, saboda kasar tana cikin yaki.
A cewarsa, akwai bukatar a sanar wa Obi alkamar kasar Ukraine, inda ya ce kasar Masar da dade tana amsar tallafi daga Ukraine kafin Nijeriya ta fara amsa.