Dan wasan gaban Nijeriya mai buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta SSC Napoli, Victor Osimhen ya rattaba hannu abkan sabon kwantiragi a kungiyar wanda zai sa ya zauna har zuwa shekarar 2026.
Napoli, mai rike da kofin Seria A, ta yi wannan sanarwar a ranar Asabar game da dan wasan Nijeriya Victor Osimhen.
- Dole Mu Yi Taka-tsantsan Wajen Fitar Da ‘Yan Wasan Da Za Su Wakilci Nijeriya A AFCON – Peseiro
- Manyan Abubuwa 5 Da Ke Kawo Nakasu Wajen Koyon Ilimi (2)
Kulob din ya bayyana cewa Osimhen ya amince da tsawaita kwantiragin, inda zai ci gaba da zama a Napoli har zuwa shekarar 2026.
Sanarwar ta fito ne ta shafin sada zumunta na Napoli, inda kungiyar ta saka hoton Osimhen yana kulla sabuwar yarjejeniya tare da mai kungiyar Aurelio De Laurentiis.