Ɗan takarar zaɓen shugaban ƙasa na PDP a 2023, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa jam’iyyar sa kaɗai ce mai wani karsashin lashe zaɓe a yanzu.
Ya ce APC, jam’iyyar da ta kassara ƙasar nan har ta kusa durƙusar da ita, za ta ɓace, a neme ta a rasa bayan zaɓen 2023.
Atiku ya yi wannan tsinkayen lokacin da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen sa ya ƙaddamar da Kwamitin Matasa na Yaƙin Neman Zaɓen PD (PDP-NYCN), ranar Alhamis, a Abuja.
“Maganar gaskiya, PDP kaɗai ce jam’iyya a Nijeriya. APC wani gungu ne kawai, kuma za mu yi nasarar korar su a ranar zaɓe. Mutuwa murus jam”iyyar za ta yi idan mu ka kore su daga kan mulki,” haka ya shaida wa matasa a wurin ƙaddamarwar.
“PDP za ta bai wa ɗimbin matasa dama a ƙasar nan, ba tare da yin la’akari ko nuna bambancin gida, arziki ko talaucin iyayen kowane matashi ba. Ko ɗan talaka ko ɗan wanene kai, PDP za ta taimake ka har ka cimma kyakkyawan ƙudirin ka a rayuwa.
“Kai ko da Atiku ya kammala wa’adin sa ya sauka, to wani Atiku ɗin zai hau,” haka tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa daga 1999 zuwa 2007 ya jaddada.
Daga nan kuma ya hori PDP-NYCN su shiga ko’ina a faɗin ƙasar nan su wayar da kan matasa kafin zaɓe.
“Ku je ku ba su tabbaci, ku ƙarfafa masu guiwa da zukata. Ku nuna masu cewa duk matsalar da APC ta jefa ƙasar nan, har yanzu ana fatan maida ta kan turbar bunƙasa. Ku ɗauki wannan aiki da gaske, ku jajirce. Shi ne damar da za ku samu nan gaba, kuma shi ne damar iyalin ku da ƙasar ku.
“Saboda haka ina umartar ku da yin aiki tuƙuru domin ku ceto ƙasar nan, ta hanyar haɗa kan dukkan ‘yan Nijeriya, musamman musamman magoya bayan PDP.”