Gabanin zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun dokoki na Jihohi a ranar 11 ga Maris, 2023, alamu sun nuna cewa jam’iyyun adawa a jihar Kwara za su hadewa jam’iyyar APC mai mulki kai.
LEADERSHIP ta rahoto cewa jam’iyyar APC ta lashe dukkan kujerun majalisar dattawa da na wakilai 9 a zaben da aka gudanar a jihar a ranar Asabar da ta gabata. Jam’iyyar ta kuma lashe zaben shugaban kasa a dukkan kananan hukumomi 16 na jihar.
Da yake jawabi a wajen taron gangamin da aka shirya domin bayyana manufofin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP Alh. Abdullahi Yaman, shugaban jam’iyyar a jihar, Hon. Babatunde Mohammed, ya bukaci magoya bayan jam’iyyar PDP da su ci gaba da kulla kyakkyawar alaka da ‘ya’yan sauran jam’iyyun siyasa a jihar, amma ban da jam’iyyar APC.
A wajen taron da aka gudanar a Ilorin, babban birnin jihar, shugaban jam’iyyar PDP, ya ce akwai yiwuwar dukkan jam’iyyun adawa su hada kai domin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihar da ke tafe.
Mohammed ya bayyana cewa, PDP itace babbar jam’iyya a jihar kuma za ta fito da karfinta a zagaye na gaba na zaben gwamna da na ‘yan majalisu a jihar.