Jagoran marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, Abba Moro, ya bayyana cewa ana tattaunawa da Peter Obi da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan domin su koma jam’iyyar PDP tare da yi mata takarar shugaban ƙasa a 2027.
Moro ya ce wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar suna kiran Obi da ya dawo PDP tare da yiwuwar zama ɗan takara.
- Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya
- Hukumar NRC Ta Dakatar Da Zirga-zirgar Jiragen Kasa Na Abuja zuwa Kaduna
Haka kuma ya tabbatar cewa ana tattaunawa da Jonathan kan yiwuwar sake tsayawa takara.
Jonathan, wanda ya shugabanci Nijeriya daga 2010 zuwa 2015, ya daina shiga harkokin siyasa tun bayan da Muhammadu Buhari ya kayar da shi.
Obi kuwa ya fice daga PDP a 2022, inda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar Labour Party a 2023, amma ya zo na uku a zaɓen.
Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa dawowar Jonathan ko Obi na iya sauya tsarin PDP wajen fafatawa da jam’iyyar mai mulki ta APC.
Jonathan na da magoya baya masu tsayi da suka daɗe a PDP, yayin da Obi kuma ya fi jan hankalin matasa.
Sai dai har yanzu akwai tambayoyi kan ko za su amince da wannan kira, da kuma yadda PDP za ta shawo kan matsalolin cikin gida kafin zaɓen fidda gwani.
Zuwa yanzu, babu wanda ya fito fili daga cikinsu ya tabbatar da komawarsa PDP.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp