Jam’iyyar PDP a jihar Jigawa ta ƙi amincewa da sakamakon zaɓen cike gurbi na Garki/Babura da aka gudanar a ranar Asabar, inda INEC ta bayyana ɗan takarar APC, Mukhtar Rabi’u Garki, a matsayin wanda ya yi nasara.
Mai magana da yawun PDP na jihar, Umar Kyari Jitau Madamuwa, ya bayyana cewa sakamakon ya biyo bayan nazarin yadda aka gudanar da zaɓen, wanda ya ce yana cika da take doka da karya ƙa’idojin zaɓe.
- Nasarar APC A Zaɓen Cike Gurbi Ta Tabbatar Da Sahihancin Mulkin Uba Sani – Mai Yaki
- INEC Ta Gargaɗi Ƴan Siyasa Kan Azarɓaɓin Yaƙin Neman Zaɓen 2027
Ya zargi jam’iyyar APC da amfani da dukiyar gwamnati wajen a jam’iyya tare da sayen ƙuri’u, da tsoratarwa da cin zarafin masu zaɓe. Ya ce hakan ya sanya zaɓen ya gaza kaiwa matsayin ingantaccen zaɓe a tsarin dimokuraɗiyya.
PDP ta yi kira ga magoya bayanta da ƴan kishin dimokuraɗiyya a jihar da su kwantar da hankula, tana mai tabbatar da cewa za ta bi matakan doka domin kwato abin da ta kira amanar da aka sace mata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp