Jam’iyyar PDP, ta ɗage taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) karo na 103 da aka shirya gudanarwa a ranar Laraba, 15 ga watan Oktoba, 2025.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Debo Ologunagba, ya fitar a ranar Litinin, ya ce an yanke wannan shawara ne saboda “sabbin abubuwan da ke faruwa a cikin jam’iyyar,” sai dai bai bayyana cikakkun bayanai ba.
- An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Kan Hanyarsa Ta Zuwa Ɗaukar Horo A Kwara
Ya ce, “An shirya gudanar da taron NEC na 103 a ranar 15 ga watan Oktoba, 2025, amma saboda sabbin abubuwan da suka taso, kwamitin na ƙasa (NWC) a wani taro da ya gudanar a ranar 13 ga watan Oktoba, ya amince da ɗage taron zuwa wani lokaci a nan gaba.”
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da PDP ke fuskantar sabon rikicin cikin gida, inda wasu daga cikin manyan jiga-jiganta ke ficewa daga jam’iyyar suna komawa jam’iyyar APC.
Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya koma jam’iyyar APC a ranar Talata, yayin da rahotanni ke cewa gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, da na Jihar Taraba, Agbu Kefas, na shirin komawa APC .
Wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da PDP ke shirin gudanar da babban taronta na ƙasa da za a yi a Ibadan, a Jihar Oyo, daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba.