Sabon Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Barista Nyesome Wike, ya yi watsi da duk wata yiwuwar sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki, yayin da ya ce, jam’iyyarsa PDP ta ba shi damar amincewa da tayin da shugaba Bola Tinubu ya yi masa na zama minista.
Wike, wanda shi ne dan jam’iyyar adawa daya tilo a majalisar ministocin Shugaba Tinubu, ya ce, yana ministan babban birnin tarayya Abuja ne domin ci gaban dimokuradiyya da kuma mayar da birnin kan turbarsa ta asali.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, shugaba Tinubu yayin kaddamar da shi kan karagar mulki, ya bayyana cewa, zai gudanar da gwamnatin hadin kan kasa ba wai lura da ‘yan jam’iyyarsa kadai ba. Zai nemo wadanda suka cancanta da mukami.
Ministan, a lokacin da yake ganawa da manema labarai na farko a matsayin minista, ya fitar da wasu ajanda guda 10 da suka fi mayar da hankali kan batutuwan tsaro, tsaftar muhalli, kiyaye tsarin babban birnin tarayya Abuja, samar da ababen more rayuwa, maido da korayen ganye a titunan birnin da toshe hanyoyin wawure kudaden shiga na birnin da sauransu.