Tsohon Kakakin Majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Y. Sulaiman, da tsohon mataimakinsa Umaru Dahiru Jamilu (PDP) sun sake komawa Majalisar dokokin jihar biyo bayan nasarar da suka samu a zaben cike gurbi da ya gudana a ranar Asabar.
Abubakar ya samu nasara ne kan babban abokin karawarsa na jam’iyyar APC, Khalid Abdulmalik.
- Zaɓen Cike-gurbi: NNPP Ta Yi Nasarar Lashe Zaɓen Kujeru Biyu Na Majalisar Jiha A Kano
- Minista Idris Ya Ƙaddamar Da Ƙungiyar Kakakin Labarai
Da yake sanar da sakamakon zaben, baturen zaben cike gurbin dan Majalisar Ningi, Farfesa Ahmad Abdulhameed ya ce Abubakar Y Sulaiman na PDP ya samu nasara ne da kuri’u 11,785 yayin da abokin nemansa na APC Khalid ya samu kuri’u 10,339.
Kazalika, a mazabar cikin garin Bauchi, Hon. Umaru Dahiru Jamilu na PDP shi ne ya lashe zaben cike gurbin, inda ya samu nasarar kayar da Kwamared Aliyu Ilale na jam’iyyar APC.
Baturen zaben mazabar Bauchi cikin gari, Farfesa Isma’ila Y Shehu ya ce, Umaru Dahiru Jamilu (PDP) ya lashe zaben ne da kuri’u 45,240 yayin da Abdullahi Aliyu (APC) ya samu kuri’u. 41,266.
Umaru Dahiru dai shi ne mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi kafin kotun daukaka kara ta soke nasarar da ya samu. Da wannan matakin zai sake komawa majalisa a matsayin mamba.
Haka zancen yake a mazabar wajen garin Bauchi wato Zungur/Galambi inda baturen zaben Farfesa Adamu Samaila na jami’ar ATBU ya shelanta Hon. Yusuf Ahmed na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar da kuri’u 2,233, hakan ya ba shi nasarar kayar da abokin nemansa Ibrahim Isa Yuguda na jam’iyyar APC da ya tashi da kuri’u 1,928.
Bugu da kari, kujerar dan majalisar Madada/Chinade kuwa, Baturen zaben mazabar, Farfesa Ahmed Abdulkadir ya ayyana Ala Nasiru Ahmed na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 13,920 da ya mangare babban abokin nemansa na APC Dantala Ali mai samun kuri’u 9,710.
Jam’iyyar PDP da ke mulki a jihar ta Bauchi ta lashe dukkanin kujerun ‘yan majalisun da aka gudanar a zaben cike gurbi a mazabar Zungur/Galambi, Ningi, da Madara/Chinade.
Sake zaben na zuwa ne bayan da kotun daukaka kara ta soke nasarar da ‘yan majalisun hudu suka samu a zaben ranar 18 ga watan Maris na 2023. Bayan hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben mazabun, kotun daukaka kara ta umarci INEC ta sake gudanar da zabe a rumfuna 42 da suke gundumomin zabe 16 a cikin kananan hukumomi uku na Ningi, Bauchi da Katagum bayan kalubalantar nasarar su da abokan hamayyarsu suka yi.
Sai dai bayan saken zaben dukkanin wadanda aka yi jayayya a kan kujerun su sun sake dawowa.