ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

PDP Ta Mayar Da Martani Mai Zafi Ga APC Kan Neman Ayyana Dokar Ta-ɓaci A Zamfara

by Leadership Hausa and Sulaiman
1 year ago
PDP

Jami’iyyar PDP a Jihar Zamfara, ta bayyana kiran da jam’iyyar APC ƙarƙashin jagorancin tsofaffin Gwamnanonin jihar, Bello Matawalle da Sanata Abdulaziz Yari suka yi na ayyana dokar ta-baci a jihar a matsayin “hassada” da ci gaban da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal.

 

A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran Jami’iyyar PDP na Zamfara, Halliru Andi ya fitar a ranar, 22 ga Satumba, 2024, ta ce, “Gwamnatin PDP ta mayar da hankali ne wajen gyara kura-kuran da gwamnatocin baya suka tafka na tsawon shekaru a jihar.

ADVERTISEMENT
  • Zamfara Ta Bayar Da Gudunmawar Miliyan 100 Ga Waɗanda Ambaliya Ta Shafa a Borno 
  • Gwamnatin Zamfara Ta Tabbatar Da Mutuwar Mutane 40 A Hatsarin Kwale-kwale

“Kiran a kafa dokar ta-baci ba shi da tushe balle makama kuma rashin mutunta al’ummar jihar Zamfara ne. Jam’iyyar APC ta yi biris da abubuwan da suka shafi tsohon Gwamna Bello Matawalle, wanda rashin sanin makamar aikin sa ne ya ƙara dagula harkar tsaro a jihar.

 

LABARAI MASU NASABA

Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso

NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Halaka Da Dama

“Rashin tabbatar da tsaro da gwamnatinsa ta yi ya samo asali ne yayin da ta riƙa ƙirƙirar samar wa ’yan ta’adda da wurin zama da sunan “sulhu”, ciki har da bayar da motocin Hilux da kuma tukuicin kuɗi ga ’yan bindigar, tare da ba su damar shiga gidan gwamnati kai tsaye. Wannan ya sa al’ummar Zamfara suka gamu da mugun nufi na wannan sakaci, inda ’yan bindiga ke afka wa al’umma sannan su koma su fake a bayan masu mulki.

 

“Ikirarin rashin gaskiya na cewa, Gwamna Dauda Lawal na yin zagon ƙasa a yaƙin da ake yi da ’yan bindiga a Jihar Zamfara, wani yunƙuri ne na siyasa domin kawo cikas ga ƙoƙarin da muke yi na magance matsalar rashin tsaro a jihar,” in ji sanarwar.

 

Ta ƙara da cewa, “Gwamna Lawal shi ne na farko a tarihin jiharmu da ya ba da fifiko kan harkokin tsaro tare da jajircewa na gaskiya, sabanin yadda gwamnatocin APC da suka shuɗe suka yi.

 

“Ba kamar jam’iyyar APC da ta siyasantar da matsalar rashin tsaro ba, gwamnatin PDP ta himmatu wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Zamfara. Nasarorin da muka samu a kan ‘yan bindiga sun samo asali ne daga jajircewar Gwamna Lawal, na ƙin yin sulhu da masu laifi. Wannan matsaya mai ƙarfi ta kafa tabbataccen alƙibla a yaƙinmu da ‘yan ta’addan.

 

“Gwamnatin PDP ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta ɗauki muhimman matakai da suka haɗa da kafa Rundunar Tsaron Kare Al’umma ‘Askarawan Zamfara’ (CPG) da kuma samar da asusun kula da tsaro domin tallafawa jami’an tsaro. Makonni kaɗan da suka gabata Gwamna Lawal ya raba motoci domin inganta ayyukan hukumomin tsaro, inda ya nuna jajircewarsa kan wannan lamari mai matuƙar muhimmanci,” in ji sanarwa.

 

Sanarwar ta ce, “Zargin da APC ke yi, farfaganda ce kawai. Ko kaɗan tsohon Gwamna Matawalle bai bayyana aniyar haɗa kai da Gwamna Lawal wajen magance matsalar rashin tsaro ba. Bugu da ƙari, Matawalle, wanda yanzu shi ne ƙaramin ministan tsaro, ya nuna rashin ƙwarewa da kuma rashin tausayawa ga al’ummar Zamfara. Tattaunawar da ya yi a asirce da ’yan bindiga, ba tare da sanin Gwamna Lawal ba, kai tsaye ya ruguza tsayuwar gwamnatin da ta yi hannun riga da batun yin sulhu da ‘yan bindiga. Bayan rashin nasarar wannan tattaunawar, ya yi ikirarin ƙarya cewa Gwamna Lawal ya amince da Naira biliyan 1.3 a cikin wata takarda da aka ƙirƙira domin sulhuntawa da ’yan ta’adda, magana mara tushe.”

 

Ta ce, “Muna kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya kori Bello Matawalle daga muƙaminsa na ƙaramin ministan tsaro. Rashin amincinsa da rashin cancantar wannan matsayi ya bayyana ƙarara a cikin ayyukan da ya yi a baya, wanda ba kawai ya lalata yaƙin da ake yi da ‘yan binidiga a halin yanzu ba ne, har ma kawo haɗari ga lafiyar ‘yan ƙasarmu. Ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta binciki matakan da Matawalle ya ɗauka, musamman alaƙar sa da shugabannin ’yan bindiga, waɗanda ke zama cikas ga shugabanci nagari.”

 

“A ƙarshe muna kira ga jam’iyyar APC da ta mayar da hankali kan al’amuran da suka shafi jihar Zamfara, maimakon yin tuhume-tuhume da karkatar da hankalin al’umma. Gwamna Dauda Lawal dai ya tsaya tsayin daka kan ƙudirinsa na kawo sauyi a jihar, kuma ba zai sa ya yi ƙasa a gwiwa ba da ikirarin da ‘yan adawa ke yi. Al’ummar Zamfara na buƙatar zaman lafiya, kuma wannan gwamnati ta himmatu wajen ganin ta cika wannan alƙawarin da ta ɗauka,” in ji sanarwar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yanzu Satar Da Kuka Yi Ba Ta Da Amfani: Kwankwaso Ga Gwamnonin APC
Manyan Labarai

Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso

November 15, 2025
NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Halaka Da Dama
Manyan Labarai

NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Halaka Da Dama

November 15, 2025
Masu Kokarin Kashe Kansu Na Kara Karuwa A Nijeriya
Labarai

Masu Kokarin Kashe Kansu Na Kara Karuwa A Nijeriya

November 15, 2025
Next Post
An Gudanar Da Bikin Da Ya Shafi Makamashi Na Nan Gaba A Birnin New York

An Gudanar Da Bikin Da Ya Shafi Makamashi Na Nan Gaba A Birnin New York

LABARAI MASU NASABA

An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka

An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka

November 15, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Yi Taka-tsantsan Da Batun Yankin Taiwan 

Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Yi Taka-tsantsan Da Batun Yankin Taiwan 

November 15, 2025
Illolin Neman Kudi Ido Rufe Ba Tare Da Kula Da Halal Ko Haram Ba

Illolin Neman Kudi Ido Rufe Ba Tare Da Kula Da Halal Ko Haram Ba

November 15, 2025
Jakadan Sin A Japan Ya Bayyana Matukar Adawa Da Kalaman Firaminista Takaichi Dangane Da Kasar Sin

Jakadan Sin A Japan Ya Bayyana Matukar Adawa Da Kalaman Firaminista Takaichi Dangane Da Kasar Sin

November 15, 2025
Yanzu Satar Da Kuka Yi Ba Ta Da Amfani: Kwankwaso Ga Gwamnonin APC

Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso

November 15, 2025
Yadda Ake Miyar Margi (Margi Special)

Yadda Ake Miyar Margi (Margi Special)

November 15, 2025
Yadda Za Ku Gyara Kanku

Yadda Za Ku Gyara Kanku

November 15, 2025
NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Halaka Da Dama

NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Halaka Da Dama

November 15, 2025
Masu Kokarin Kashe Kansu Na Kara Karuwa A Nijeriya

Masu Kokarin Kashe Kansu Na Kara Karuwa A Nijeriya

November 15, 2025
Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa

Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa

November 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.