Rigimar shugabanci a jam’iyyar adawa ta PDP, ta lafa yayin da Sanata Samuel Anyanwu ya samu umarnin komawa bakin aikinsa a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa.
Muƙaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Umar Damagum, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Laraba a hedikwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza, Abuja.
- Gwamnan Sakkwato Ya Kaddamar Da Aikin Gina Gidaje 500 Don Rage Matsalar Rashin Gida
- KAROTA Ta Kama Matasa 5 Kan Ɗaukar Bidiyo A Kan Hanya A Kano
Damagum ya kuma bayyana cewa an soke taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) karo na 100 da aka shirya yi, saboda wasu matsaloli.
ADVERTISEMENT
Maimakon haka, jam’iyyar za ta gudanar da wani taro a ranar 30 ga watan Yuni, wanda shi ne ranar da aka fara tsara babban taron nata.














