Da safiyar yau Laraba, mai dakin shugaban kasar Sin Peng Liyuan, ta gayyaci matan shugabanni mahalarta taron dandalin tattauna hadin gwiwar kasa da kasa, kan shawarar ziri daya da hanya daya ko BRF karo na uku da aka kaddamar a yau, zuwa gidan adana kayayyakin fasaha na kasa dake nan birnin Beijing.
Wadanda suka ziyarci gidan adana kayan fasaha tare da Peng Liyuan, sun hada da matayen shugabannin kasashen Indonesia, da Kenya, da Laos, da Serbia, da Sri Lanka, da Turkmenistan, da Uzbekistan. Sauran su ne na Cambodia, da Hungary, da Papua New Guinea. (Mai fassara: Saminu Alhassan)