Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi, ya kai ziyarar ta’aziyyar ne ga iyalan marigayi dattijon ƙasa kuma ɗan kasuwa, Alhaji Aminu Dantata, a gidansu da ke Kano ranar Laraba.
A yayin ziyarar, Obi ya bayyana marigayin a matsayin wani gagarumin ginshiƙi a harkokin tattalin arziƙin Nijeriya, yana mai cewa: “Mun zo nan yau domin jajanta wa iyalan marigayi da kuma ɗaukacin al’ummar ƙasar nan, domin wannan rashin ya shafi kowa. Alhaji Aminu Dantata ba kawai ɗan kasuwa ba ne, ya gina rayuwar mutane da dama kuma ya kula da kowa cikin tausayi.”
- Mai Tsaron Ragar Nijeriya, Peter Rufai Ya Rasu
- Gwamna Peter Mbah Ya Ƙaddamar Da Jiragen Kasuwanci 3 Na ‘Enugu Air’ Mallakin Jihar
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya yaba da irin rayuwar da Dantata ya yi, yana mai cewa: “Ya bar babban abin koyi, ba kawai a kasuwanci ba, har ma a gina mutane. Rayuwarsa abin koyi ce kuma za ta ci gaba da ba mu sha’awa.”
Obi ya kuma yi addu’ar Allah ya gafarta wa marigayin, ya saka masa da alheri, tare da bai wa iyalansa ƙarfin gwuiwa da juriyar rashin nasa.
Alhaji Aminu Dantata ya rasu ne a ranar 28 ga Yuni, 2025 a wani asibiti da ke Abu Dhabi, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), kuma an binne shi a birnin Madina, Saudiyya kamar yadda ya buƙata kafin rasuwarsa. Har yanzu ana ci gaba da samun saƙonnin ta’aziyya daga faɗin Nijeriya bisa gudummawar da ya bayar ga ci gaban kasuwanci da Nijeriya baki ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp